A Cire Tsoro a yi Abinda ya Kamata: Dalilin da Yasa na Wallafa Bidiyon Pantami – Aisha Buhari
Mai dakin shugaban kasan Najeriya, Aisha Buhari ta bayyana dalilin da ya sa tayi amfani da bidiyon ministan sadarwa Ali Isa Pantami wurin bayani ga ‘yan Najeriya.
A cewar ta ta wallafa bidiyon ne don kwatanta wa ‘yan Najeriya abubuwan da suke faruwa dangane da yaƙi kan rashin tsaron da ke kasa.
Aisha Buhari ta wallafa bidiyonsa ne yayin da yake wa’azi yana rusa kuka saboda kashe-kashen da ake yi a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.
FCT, Abuja – Uwar gidan shugaban Buhari, Aisha Buhari ta bayyana kwararan dalilan ta na amfani da bidiyon ministan sadarwa, Ali Isa Pantami don kwatanta wa ‘yan Najeriya abubuwan da suke faruwa na matsalolin rashin tsaro a kasar nan.
Read Also:
Matar shugaban kasan ta wallafa bidiyon ministan wanda dama malamin addinin musulunci ne yana koyar da mutane tare da yin wa’azi dangane da kashe-kashen da ake yi a Najeriya a lokacin mulkin shugaban kasa Goodluck Jonathan inda ya ce shi Ubangiji kadai yake tsoro ba mutum ba.
Wallafa bidiyon da yin tsokaci akan shi ya janyo cece-kuce sosai
Kamar yadda Aisha Buhari tayi tsokaci akan bidiyon Pantami a wallafar ta ta ranar Lahadi inda ta sa:
“A cire tsoro a yi abinda ya kamata”.
Wannan wallafar ta janyo cece-kuce inda har wasu suke cewa tana bayyana gazawar mulkin mijinta kamar yadda ta dade tana yi tsawon shekaru
Bayan surutai sun yawaita ne ta kara wata wallafar yayin da ta faɗaɗa bayani dangane da wallafar ta ta farko. Ta ce ta yi amfani da bidiyon ne don ta bayyana yadda yin abinda ya dace ba tare da tsoro ba yake haifar da da mai ido.
Kamar yadda Aisha Buhari ta yi wallafar ta biyu a ranar Litinin, a shafinta na Instagram:
“Tafsir din Malam akan tsoron Allah ba na mutum ba. Bayan an cire tsoro da son kai an shiga Zamfara, abubuwa sun fara kyau, sai a dage a shiga sauran wurare haka”