Dalilan da ya sa ƴan siyasa ke barin APC – Ndume

 

Abuja – Sanata Muhammed Ali Ndume ya bayyana cewa ba shi shirin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa SDP.

Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa Najeriya ya ce jiga-jigan APC da ke shirin sauya sheka an fusata su ne.

Sanatan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a, 11 ga watan Afrilun 2025 a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels tv.

Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya tattara ya bar APC, tare da komawa jam’iyyar SDP mai alamar doki.

Tun bayan sauya shekar El-Rufai, manyan jiga-jigai daga APC da sauran jam’iyyun siyasa a Najeriya suka mara masa baya, suka fara rungumar SDP.

Akwai raɗe-raɗin da ake cewa tsofaffin ministocin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na shirin haɗewa da El-Rufai a SDP.

Ali Ndume na shirin komawa SDP?

Da aka tambaye shi ko yana da shirin komawa SDP, Sanata Ali Ndume ya ba da amsa da “a’a.”

Ya ce bai da wani shiri na sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa SDP ko PDP, duk da ce-ce-ku-cen da ke kara yaduwa game da yuwuwar ƴan CPC na barin jam’iyyar.

Sai dai ya ce APC na da dalilan damuwa idan lamarin ƴan CPC da ake zargin su na shirin komawa SDP ya tabbata, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

“Ba za a yi biris da irin wannan barazana ba. Kowace kuri’a na da muhimmanci,” in ji shi.

Dalilan da ya sa ƴan siyasa ke barin APC

Ndume ya ce dalilin da yasa wasu fitattun ‘yan siyasa ke shirin ficewa APC shi ne saboda ba a kula da bukatunsu ko saka su cikin tafiyar gwamnatin da suka taimaka aka kafa ba.

“Idan ba a biya wa mutane buƙatunsu ba, sai ka ga sun sauya sheka, musamman a Najeriya, za ka ga ƴan siyasa na tsalle-tsalle tsakanin jam’iyyu kuma ba su damu ba. Ndume ya kara da cewa gazawar gwamnatin APC na jawo waɗanda suka taimaketa ta samu nasara, na daga cikin abubuwan da ke fusata ƴaƴan jam’iyyar.

“Shekaru biyu kenan da muka kafa gwamnati, amma mutane da dama na jin an watsar da su, ba sa samun damar ganin shugaban kasa.”

Sanata Ndume ya ankarar da Tinubu

Ya kuma bayyana yadda aka maida martani mai zafi gare shi lokacin da ya yi kokarin sanar da shugaban kasa game da halin da ake ciki:

Maimaikon a saurari sakon, sai aka fara zagin mai sakon a jaridu. Wannan matsala ce babba, kuma tana da matukar hatsari,” in ji Ndume.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here