Dalilin da Yasa na Koma APC – Shugaban Jam’iyyar PDP na Jahar Ebonyi

 

Onyekachi Nwebonyi, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jahar Ebonyi ya ce ya yi farin cikin komawa APC.

Nwebonyi, ya ce rashin adalci da ake yi wa Ibo da wasu dalilan ne suka saka shi ya fice daga jam’iyyar.

Tsohon shugaban na PDP ya ce Ibo sun bada gudunmawa sosai wurin gina PDP amma da lokacin basu damar takarar shugaban kasa ya yi sai aka hana su Tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jahar Ebonyi, Onyekachi Nwebonyi ya ce ya yi farin cikin ficewa daga jam’iyyar, inda ya ce rashin adalci na daga cikin dalilin da yasa ya fice, rahoton Vanguard.

Nwebonyi, yayin bikin tarbarsa da aka yi a Abakaliki bayan gwamnan jahar David Umahi ya nada shi a matsayin kwamishinan babban birnin jahar Abakaliki, ya kara da cewa rashin bawa yankin kudu takarar 2023 alama ce da ke nuna suna nunawa Ibo bangaranci.

“Na yi farin cikin barin PDP saboda cike take da rashin adalci. Kana iya ganin jam’iyyar bata yi wa ibo adalci. “Ka tuna, Ibo ne suka bada gudunmawa kashe 70% wurin kafa PDP a 1998, mun yi wa jam’iyyar hidima sosai.

“Muna taka rawar da ya kamata mu yi a jam’iyyar wurin zabe amma da lokacin mu ya yi a 2023 sai jam’iyyar ta ce babu tikiti. “Me yasa sai da lokacin ibo ya zo sannan za ku ce kowa na iya takarar, lokacin kudu maso yamma, kun basu, lokacin arewa, kun basu.

“Yanzu da lokacin kudu maso gabas ya yi, kuma kuna cewa ba za a cigaba da karba-karba ba, wannan ai yaudara ne,” in ji shi. Tsohon shugaban na PDP ya yi wa gwamnan godiya saboda bashi mukamin kwamishina na babban birnin jahar wato Abakaliki.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here