Dalilin Ziyarar da Muka Kai wa Ganduje – Alhassan Rurum

 

Wasu ‘yanmajalisar tarayya na jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano sun bayyana dalilin wata ziyara ta musamman da suka kai inda suka gana da shugaban jam’iyyar APC na Najeriya, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Ƴanmajalisar sun haɗa da Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila da danmajalisar wakilai Hon Kabiru Alhassan Rurum da danmajalisa mai wakiltar Dala Ali Madaki da tsohon dan majalisar tarayya wakilai Badamasi Ayuba.

A tattaunawar da ya yi da BBC bayan ganawar da suka yi da shugaban jam’iyyar ta APC, Kabiru Alassan Rurum, ya ce sun yanke shawarar kai wa Ganduje ziyarar ne wadda ya ce ta musamman ce bisa matsayinsa a kasa da kuma kasancewarsa jigo daga jihar da suke wakilta a tarayya wato Kano.

”Mun kai ziyara ta musamman ta ban-girma ga shi maigirma shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

”Kuma dama muna da alaka ta kusa tsakaninmu illa al’amura na siyasa in ya taso akan iya samun bambancin ra’ayi ko da gida daya ake,” in ji shi.

Danmajaisar ya ce saboda lokaci ya fara kankama na tunkarar siyasar da ke tafe ta 2027, ya dace su fara tattaunawa, kamar yadda sauran ‘yansiyasa a matakai daban-daban na kasar suke ziyarce-ziyarce na neman shawara daga manya da hada tafiya da wadanda suke ganin za su kai ga cimma muradinsu na siyasa na jiha da kuma kasa, a matsayinsu na wakilan jihar ta Kano.

Rurum ya ce tattaunawar tasu ta yi kyau kuma sun tsayar da lokacin sake ganawa domin ci gaba da ita kafin su fito da matsaya kan abin da suka zartar game da alkiblar da za su dosa a siyasarsu ta jiha da ma tarayya.

Duk da cewa da dama ana yi wa wannan ganawa tasu da shugaban jam’iyyar ta APC a matsayin wani shiri na sauya sheka daga jam’iyyarsu ta NNPP zuwa APC, Honarabul Rurum ya ce, sun dai fara wannan tattaunawa ne daga gida kasancewar Ganduje daga jihar Kano, kuma kofarsu ya ce a bude take su tattauna da kowace kungiya ko jam’iyya ko wani bangare na siyasa.

Game da jita-jitar da ake yi cewa ko za su koma jam’iyyar ta APC ne sai ya ce, “ai ita dumukuradiyya tsari ne na hadaka tsakanin bangarori daban-daban a hada karfi da karfe domin a kai ga nasara.”

”Hannu daya ba ya daukar daki saboda haka babu mamaki a ga mun hade da jamiyyar APC, babu mamaki ko da jam’iyyar PDP za mu hade kuma babu mamaki mu yi zamammu a matsayinmu na masu jam’iyya sabuwa fil NNPP mai kayan marmari, duk komai na iya kasancewa a siyasar nan,” a cewar danmajalisar.

Rurum wanda ya kasance tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano, ya ce, kamar yadda ‘yansiyasa da dama a yanzu suka shiga laliben abokan burmi, ”muma a matsayinmu na zaratan ‘yansiyasa muka ga lokaci ya yi mu ga cewa da wadanne irin mutane ya kamata yanzu a zo a buga sabuwar siyasa ta 2027, in Allah Ya kai mu.”

Zargin yi wa NNPP ko Kwankwaso butulci

adda ake ganin wadannan jiga-jigan ‘yanmajalisa na tarayya daga jihar ta Kano sun samu matsayin da suke kai ne a yanzu ta hanyar jam’iyyar NNPP ( Kwankwasiyya), bayan sun rasa takara tare da batawa da jam’iyyarsu ta baya APC, komawarsu tsohuwar jam’iyyar a yanzu na zama kamar wani butulci a wajen wasu.

A kan masu yi musu wannan kallo, ‘yansiyasa na ganin cewa wannan ba butulci ba ne a cewar Rurum : ”Ai a siyasar kasar nan ba abin da bai faru ba, ba kuma abin da ba ya faruwa.

”Kuma dukkan wani babba, jagora a cikin jam’iyyar nan ba wanda daga wata jam’iyya yake ya fita wata ba.”

Ya kara da cewa,” ita kanta jam’iyyar APC haduwa aka yi da CPC da APP da sauran PDP aka kafa ta saboda haka lokaci yanzu na tattaunawa a hada tafiyar da za ta ciyar da jihar Kano gaba kuma ta ciyar da Najeriya gaba.

”Bugu da kari a sha’anin gwamnati da siyasa, akwai wanda yanzu da shi aka gama wahala a zaben Bola Ahmed Tinubu, amma yau ba sa tare da shi, akwai kuma wadanda ba a yi da su yau suna tare da shi.

Saboda haka ita maganar siyasa a kasar nan abu ne na ra’ayi da manufa, daga ina kake kuma ina za ka je, kuma ina ne kake ganin idan kuka hadu za ka kai gaci.” In ji shi.

Jita-jitar komawar Kwankwaso APC

Kasancewar wasu na jita-jitar shi kansa jagoran jam’iyyar NNPP, kuma tsohon gwamnan jihar ta Kano, Rabiu Musa Kwankwaso zai koma jam’iyyar ta APC, BBC ta tambayi Honarabul Rurum ba ya ganin idan a karshe suka yanke shawarar komawa APC, shi ma kuma Kwankwason ya koma za su sake haduwa a can, sai ya ce : ” kamar irin zaman aure ne za ka ga mutum mutum daya yana da mata 3 ko mata hudu in mace ta yi hakuri ta zauna da mijinta.

”Saboda haka idan Allah Ya sa tafiya ta sake hada mu a i duk uwa daya uba daya muke. Daman tun a farko mun yi tafiya tare.

”Mun yi PDP da shi muka zo muka yi APC, muka yi NNPP to ba mamki tun da siyasa ce za mu iya sake haduwa wa ni guri, illa idan aka hade ya san halina na san halinsa.

Zuwa yanzu dai jam’iyyar NNPP ba ta ce komai ba dangane da zargin neman sauya shekar wadannan jiga-jigan ‘yansiyasa kuma ‘yanmajalisar tarayyar na jihar Kano, daga NNPP zuwa APC mai mulkin kasar.

Amma kuma wasu bayanai na nuni da cewa komai zai iya bayyana nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here