‘Dan Kungiyar Kwallon Kafar Nasarawa United ya Bace

Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta sanar da bacewar dan wasanta Muhammad Hussain.

Shugaban kungiyar na Nasarawa United Isaac Danladi ne ya sanar da haka a ranar Laraba a garin lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa.

Kungiyar ta gargadi duk wani mutum ko kungiya da ke shirin dauke dan wasan da ta yi hattara saboda har yanzu yana da ragowar kwantaragi.

Hukumar Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta sanar da cewa daya daga cikin yan wasan ta, Muhammad Hussain, ya bace, kuma ba a san inda ya ke ba.

Shugaban kungiyar Nasarawa United, Isaac Danladi ne ya bayyana haka ranar Laraba a garin Lafia, ta kafafen yada labaran kungiyar, The Punch ta ruwaito.

Danladi ya bayyana cewa dan wasan ya na da ragowar kwantaragi da kungiyar kuma ya na karbar albashin sa duk wata har kawo yanzu, kafin a neme shi a rasa.

Ya kara da cewa Hussain bai dawo kungiyar ba tun barowar su filin atisayen Flying Eagles, bayan cire su daga kofin zakarun Afirka na yan kasa da shekara 20 a kasar Benin a baya bayan nan.

Shugaban kungiyar ya gargadi duk wani mutum ko wata kungiya da ke shirin dauke dan wasan daga kungiyar da ya yi hattara, ya na mai cewa sun sanar da hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF da kuma hukumar shirya gasar firimiya halin da ake ciki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here