Sanata Ibrahm Abdullahi Danbaba ya Sauya Sheka daga PDP Zuwa APC

 

Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba, sanata daga jihar Sokoto ya bayyana ficewarsa daga PDP zuwa APC.

Sanatan ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya mika wa shugaban majalisar dattawa a yau Laraba.

Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa ne ya bayyana hakan a zaman majalisar da aka yi a yau 27 ga watan Afrilu.

FCT Abuja – A yau ne majalisar dattawa ta sanar da cewa, Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Danbatta ya mika wasika ga shugaban majalisa, inda shugaban ya karanta ficewar sanatan daga PDP zuwa APC a zaman majalisar na yau Laraba 27 ga watan Afrilu.

Sanarwar ta Legit.ng Hausa ta samo daga majalisar ta ce:

“Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya karanta wasikar Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Ibrahim Abdullahi Danbaba, inda ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki.”

Yayin da APC ke ci gaba da jiran ranar zaben fidda gwani, jam’iyyar na ci gaba da samun bakin fuska cikinta a ‘yan kwanakin nan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here