Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya Sayi Fom din Takarar Shugaban Kasa Karkashin Jam’iyyar APC

 

Karamin Ministan ilimi, Hanarabul Chukwuemeka Nwajiuba, ya sayi Fom din takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress APC N100m.

Nwajiuba ya sayi Fom din ne a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu, a hedkwatar uwar jam’iyyar APC dake birnin tarayya Abuja.

Legit ta samu labari ne daga bakin hadimin shugaban majalisar dattawa kan sabbin kafafen yada labarai, Abubakar Siddiq Usman.

A cewarsa, wasu yan Najeriya ne suka hada masa kudi milyan dari kuma suka saya masa Fam din.

A cewarsa:

“Karamin Ministan Ilimi, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba, ya zama mutumin farko da ya sayi Fom na takarar zaben fidda gwanin jam’iyyar APC yayinda wasu yan Najeriya suka tara sama da N100m don saya masa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here