Fitaccen Mai Yin Barkwanci a Kafafen Sada Zumunta, Dan Bello ya yi Rijiyar Burtsatse a Katsina

 

Jihar Katsina – Fitaccen mai yin barkwanci a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Dan Bello, ya yi abin a yaba bayan ya kammala aikin rijiyar burtsatse.

Rahotanni sun nuna cewa Dan Bello ya yi rijiyar burtsaye mai amfani da hasken rana a ƙauyuka biyu na jihar Katsina.

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka tona rijiyar ne a cikin wani bidiyo da Dan Bello ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dan Bello: Kalubale ga Buhari da Sirika

Ƙauyukan da aka gina rijiyar sun haɗa da Yar Lami Santar Riga da Yar Lami Santar Lema, waɗanda ke kusa da mahaifar shugaba Muhammadu Buhari.

Haka zalika kauyukan suna kusa da mahaifar tsohon ministan harkokin sufurin jiragen saman Najeriya, Hadi Sirika.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa aikin ya taimaka wajen rage wa al’ummar da suka daɗe suna fama da matsalar rashin tsaftataccen ruwan sha wahala.

Hakan ya sanya ake ganin aikin kalubale ne ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Hadi Sirika.

Rashin ruwan sha a kauyukan Katsina

Kafingagarumin aikin da Dan Bello ya aiwatar, mazauna waɗannan ƙauyuka sun kasance suna tafiya sama da awa ɗaya domin samo ruwan sha daga wani tafki mai datti.

Matsalar ta shafi rayuwar yara da manya, inda yara ke kasa zuwa makaranta saboda wahalar da ake sha wajen samun ruwa.

Fadi tashi wajen tona rijiyar burtsate

A yayin da Dan Bello ya fara aikin rijiyar, ya fuskanci kalubale bayan na’urar tono rijiyar ta kasa cimma ruwa duk da an toni kasa har mita 65.

Matsala ta sa jama’ar ƙauyukan suka soma jin shakku, ganin yadda shugabannin siyasa da dama suka musu alkawuran da ba su cika ba a baya.

Duk da haka, Dan Bello bai karaya ba, ya ci gaba da kokari har ya kammala aikin. A ranar 1 ga watan Fabrairu, an kaddamar da rijiyar wacce ke samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar.

A ina Dan Bello ya samo kudin aikin?

Dan Bello ya bayyana cewa kuɗin aikin rijiyar ya fito ne daga ribar da yake samu ta hanyar tallace-tallacen bidiyonsa a kafafen sada zumunta.

“Wannan aiki ba zai yiwu ba da ba tare da goyon bayan masoyana a kafafen sada zumunta ba.

– Dan Bello

Ya ƙara da cewa ya dauki wannan aiki a matsayin wani alhakin jagoranci na gaskiya da ya kamata duk wani ɗan Najeriya ya nuna, musamman shugabanni.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here