‘Dan Bindiga ya Kashe Mutane 6 a Jami’ar Perm Dake Rasha

 

Wani dan bindiga ya kashe mutane shida a wata jami’a a Rasha.

Ƙarin wasu ashirin da hudu sun ji rauni yayin harin na jami’ar Perm, Urals.

Dalibai da malamai da dama sun buya a ginin jami’ar; yayin da aka ga wasu suna tsallake katanga.

‘Yan sanda sun ce sun raunata tare da tsare maharin – abun da ya saba da rahotannin da aka bayar na cewa an kashe shi.

Maharin wanda aka rawaito cewa dalibi ne ya bar sako a kafafen sada zumunta inda yake nuna tsantsar ra’ayinsa na son zubar da jini.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here