Kakakin Jam’iyyar APC Rashen Jahar Ribas ya yi Murabus Daga Mukaminsa

 

Kakakin jam’iyyar APC reshen jahar Ribas ya mika takardar murabus daga kan mukaminsa ga shugabannin jam’iyyar.

A cikin takardar mai ɗauke da kwanan watan 19 ga watan Satumba, Chief Ogbonna Nwuke, yace lokaci ya yi da zai fuskanci wasu abubuwan na daban.

Tsohon kakakin ya mika godiyarsa ga kowa da kowa na cikin jam’iyyar APC musamman mambobi waɗanda suka ba shi goyon baya.

Rivers – Kakakin jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar nan reshen jahar Ribas, Chief Ogbonna Nwuke, ya yi murabus daga kan mukaminsa, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Nwuke, ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aike wa shugabannin jam’iyyar mai ɗauke da kwanan watan 19 ga watan Satumba.

Kakakin APC na ribas ya bayyana cewa ya ɗauki matakin sauka daga mukaminsa ne a karan kansa.

Meyasa ya yi murabus?

Punch ta rahoto a wasikar da Nwuke ya aike wa shugabannin jam’iyya, yace:

“Muna da tabbacin cewa aikin da aka bamu, mun kammala shi, mun zo wannan matakin (Kakakin APC) dai-dai lokacin da yake da ƙalubale sosai.”

“Duk abinda yake da farko to yana da ƙarshe, lokaci ya yi da zamu matsa mu baiwa wasu wuri, kuma lokaci ne da ya dace mu maida hankali kan wasu abubuwan na rayuwa.”

Nwuke ya gode wa kowa a APC

Tsohon kakakin APC ya godewa abokan aikinsa a jam’iyyar APC musamman mambobin jam’iyya bisa kwarin guiwar da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa.

“Mun amfana matuka da irin goyon bayan da mambobi suke ba mu, da kuma kwarin guiwa da fatan alkairin da suka kasance suna mana.”

“Yayin da muke jiran ta Allah ta kasance da kuma tsarin da Ubangiji ya mana a rayuwa, mun yi iyakar bakin ƙoƙarin mu wajen sauke nauyin da aka ɗora mana.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here