Hatsabibin ‘Dan Boko Haram, Adamu Rugu Rugu da Iyalansa Sun Kai Kansu Gaban Sojojin Najeriya
Adamu Rugu Rugu da ‘Ya ‘yansa da mata sun hakura da yaki da sojojin Najeriya.
Rahotanni sun ce yau Rugu da Iyalinsa suka kai kansu gaban Sojoji dake Gwoza.
Mutanen Garin Gwoza duk sun san labarin irin ta’adin Amir Adamu Rugu Rugu.
Borno – Rahotanni suna nuna cewa wani babban jagoran ‘yan ta’addan Boko Haram, ya mika kansa gaban rundunar sojojin kasa na Najeriya a jahar Borno.
Adamu Hamidu ya ajiye makamai
Jaridar Daily Trust ta ce Amir Adamu Rugu Rugu ya sallama kansa tare da iyalansa ga dakarun Operation Hadin Kai da ke karamar hukumar Gwoza a Borno.
Rahoton yace Adamu Rugu Rugu da yaransa sun yi kaurin-suna sosai wajen ta’addanci a yankin dajin Sambisa da kuma tsaunukan Mandara da ke yankin Gwoza.
Read Also:
Jagoran ‘yan ta’addan ya kan tare matafiya, tare da kai wa jami’an tsaro hari a Arewa maso gabas.
Wata majiya daga gidan sojan kasan Najeriya ta tabbatar wa Daily Trust cewa Adamu Rugu Rugu ya mika kansa ne tare da matansa uku da ‘ya ‘yansa a Gwoza.
Wani mazaunin Gwoza ya shaida wa manema labarai cewa mutanen gari sun san wannan ‘dan ta’adda, ya na mai farin cikin kawowar karshen ‘yan ta’addan.
“Mun gode wa Allah, shahararren ‘dan Boko Haram, Amir Adamu Rugu Rugu, ya mika kansa yau a garin Gwoza, Karshen Boko Haram ya zo in Allah ya so.”
Sojoji sun taba cewa sun ga bayan Rugu Rugu Akwai lokacin da dakarun Operation Lafiya Dole suka bada sanarwar cewa sun kashe Adamu Hamidu, wanda aka fi sani da Adamu Rugu Rugu a farkon 2019.
Jami’in sojan da yake magana da yawun Operation Lafiya Dole a lokacin, Kanal Ado Isa, ya fitar da jawabi, ya na cewa sun ga bayan babban sojan ‘yan ta’addan.
Yerwa Express ta ce Rugu Rugu ya shiga Boko Haram ne a 2014, bayan an ci karfin garin Gwoza.