Kamfanin Matatar Man Dangote ta Dakatar da Siyar da Mai a Naira

 

Kamfanin matatar mai ta Dangote ta sanar da cewa ta dakatar da sayar da man fetur da kuɗin Najeriya wato Naira.

Kamfanin ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya aike wa dilallan man fetur a yau Laraba.

Sanarwar ta ce ”Kamfanin matatar mai ta Dangote ta dakatar da sayar da fetur a naira na wani lokaci. Hakan ya zama wajibi ne saboda kaucewa rashin daidaito da ake samu tsakanin ribarmu da kuɗin da muke sanya wa masu sayen ɗanyan mai wanda a yanzu galibi da dala muke yi.”

Kamfanin ya kuma ƙara da cewa bisa wannan dalilin, wajibi ne su sauya kuɗin da suke siyar da man domin ya yi dai-dai da kuɗin da su ke siyan ɗanyen mai na wani ɗan lokaci.

Sanarwar ta kuma ce kamfanin ya dukufa wajen biyan buƙatun kasuwannin Najeriya, kuma da zarar sun karɓi jiragen dakon mai da aka siya da Naira daga kamfanin NNPC, za su ci gaba da siyar da man fetir ɗin da Naira.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here