Kin Biyansa N25,009,243: ‘Dan Kwangila ya Kaiwa EFCC Korafin Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo Dake Jahar Kano

 

Wani dan kwangila, Mustapha Umar-Tallo ya kai wa ofishin EFCC takardu dauke da korafin shugaban karamar hukumar Gwarzo, Bashir Abdullahi da ke Kano.

Ya bayar ga korafin ne sakamakon yadda Abdullahi ya ki biyan shi kudaden kwangilar da ya kammala na karamar hukumar duk da gwamnatin jahar ta saki kudin.

Takardun sun bayyana yadda dan kwangilar ya biyo shi N25,009,243, sannan ya bayyana sauran ayyuka 12 da gwamnatin jahar ta biya kudaden su amma Abdullahi ya lamushe kudin.

Kano – Wani dan kwangila, Mustapha Umar-Tallo ya mika takardu 2 zuwa ofishin hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ya na zargin shugaban karamar hukumar Gwarzo, Bashir Abdullahi da kin biyan shi kudaden kwangilar da yayi na karamar hukumar.

Daily Nigerian ta rawaito cewa, Umar-Tallo, ya rubuta takardar ta lauyan sa, Abubakar Lagazab, inda ya ke zargin shugaban karamar hukumar da kin biyan su kudaden duk da gwamnatin jahar ta riga ta biya kudaden.

A takardar ta ranar 17 ga watan Nuwamba 2020 wacce ya bayyana ta ga manema labaran jahar Kano a ranar Alhamis, Umar-Tallo ya zargi shugaban karamar hukumar da lamushe kudaden ayyuka 20 na kwadago da ayyuka 14 na karamar hukumar.

Wani bangare na wasikar farkon ta zo kamar haka:

“Ayyukan 20 wadanda kudaden su ya kai N21,907,875 amma kuma ya biya ma N14,907,875. Mun hada wasikar da bayanan ayyukan har da na kudaden don karin bayani. “Sauran ayyukan guda 14 na N10,101,368 ma har yau bai biya mu ko sisi ba.

Yanzu gaba daya mu na bin shi N25,009,243 kuma gwamnatin jahar Kano ta dade da sakin kudin ayyukan. Idan ya na da korafi kuma zai iya kawo duk wasu takardun shaidar sa.

Dangane da yasar dukiyar jama’a kuma, takardar ta biyu mai dauke da kwanan wata 23 ga watan Nuwamban 2020 wacce ya yi irin korafin dai ta zo kamar haka:

“Yallabai, na tattaro bayanai dangane da ayyuka 12 wacce shugaban karamar hukumar Gwarzo ya amshi kudade daga hannun gwamnatin jahar Kano ya na nuna kamar ya biya amma kuma ya lamushe”.

“A bisa korafin da na yi, ayyuka 7 da na lissafo na N423,561,188 wadanda har yanzu bai yi ayyukan ba,” kamar yadda takardar ta zo.

Majiya daga ofishin EFCC ta sanar da manema labarai cewa tuni hukumar ta gayyaci shugaban karamar hukumar zuwa ofishin su don ya amsa tambayoyi, Daily Nigerian ta wallafa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here