Dan Majalisa ya Harbe Dan Fashi
Wani dan majalisar tarayya dan jahar Sokoto ya samu nasarar aika wani dan fashi lahira.
Dan majalisar ya harbe dan fashin yayain da suka shiga gidansa yin sata da ‘yan uwansa.
Rundunar ‘yan sanda ta jahar sun tabbatar da faruwar hakan, yayin da suka kai dauki gidan dan majalisan.
Wani dan majalisar wakilai, Abdullahi Balarabe Salame, ya ba da labarin yadda aka yi fashi a gidansa da ke Sakkwato inda ya harbe daya daga cikin ’yan fashin da makamin.
PM News ta ruwaito cewa dan majalisar mai wakiltar mazabar Gwadabawa da Illela na tarayya ya nuna hotuna don tabbatar da harin da ‘yan fashin suka kai.
“Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukaki.
Read Also:
“A yau da misalin karfe 3 na safe, wasu ‘yan fashi da makami sun kawo min hari a gidana da ke Sakkwato amma cikin ikon Allah, na sami damar harbi na kashe daya (dan fashin) na kuma raunata wasu. Ina godiya,” in ji dan majalisar.
Daya daga cikin hotunan da Salame ya watsa ya nuna yadda aka fasa kofar gidansa. Wani kuma yana nuna hula ‘faze cap’ ta baci da jini, takobi da kulki.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a Sakkwato, Muhammad Sadiq ya tabbatar da rahoton, inda ya ce, “‘Yan sanda sun yi hanzari don taimakawa wajen dakile harin”.
“Rundunar‘ yan sanda ta jahar Sakkwato na sane da yunkurin afkuwar fashi da makami a yankin Bado Quarters da ke Sakkwato, lamarin da ya gamu da cikas sakamakon hanzarin mayar da martani na hadin gwiwar ’yan sanda masu sintirin birane,” in ji shi a cikin wata sanarwa.