‘Dan Majalisar APC Daga Kano ya Soki Gwamna Abdullahi Ganduje

 

ya soki Gwamna Abdullahi Ganduje da manyan APC.

J ya na wakiltar / , amma an ja layi a APC.

‘Dan Majalisar ya kira Gwamna barawo, ya kuma ce bai jin tsoron kowa.

Honarabul Abdulkadir Jobe mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa da Rimin Gado a majalisar tarayya, ya fito ya na sukar gwamna Abdullahi Ganduje.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter, an ji Abdulkadir Jobe ya na yin kaca-kaca da mai girma gwamnan, har ya na kiransa da sunaye maras dadi.

Jobe ya yi kaca-kaca da masu yi masa barazana, ya ce babu wanda ya isa ya kore sa daga jam’iyya.

A wannan bidiyo da wani mai suna Hassan Umar ya wallafa a ranar 3 ga watan Junairu, 2020, an ji mabiya bayan Jobe su na yi masa kirarin ‘daram-dam.”

Saboda haka, ni ‘Dan jam’iyyar APC ne cikakke, mu na nan a APC, a APC babu wanda ya isa ya kore ni daga jam’iyya.

Jobe ya aika sakonsa na musamman zuwa ga Abdullahi Umar Ganduje, ya na ce masa ‘Kai barawo ne!’

Wasu a gefe sun amsa da cewa: (Gwamna) ya ci Dala. An dade ana zargin gwamnan Kano. Dr. Abdullahi Ganduje da laifin karbar rashawan Daloli.

Hon. Abdulkadir Jobe ya ke cewa ‘dan majalisar da ya fito daga kudancin jihar Kano ya ce: “Ina alfahari da kaina, da iyayena, da mutanen garin Dawakin Tofa.”

‘Dan siyasar ya yi ikirarin su ne masu jama’a. “Ko za a mutu, ko za ayi rai, mu na APC. Idan mutum ya ce shi ‘dan APC ne, ko waye shi, ya tsaya a fito ayi zabe.”

A karshen wannan bidiyo, za a ji ‘dan majalisar ya na cewa ya lashe zaben majalisar tarayya har sau uku: “Kowa ya san ni, ya sanni Jobe, ba mai tsoro ba ne.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here