2021: Hare-Haren da ‘Yan Bindiga Suka kai a Jahar Kaduna
Wasu ‘yan bindiga sun kai wasu jerin hare-hare a yankin karamar Giwa da ke jihar Kaduna.
Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida a Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce an fara kai hare-haren ne ranar sabuwar shekara.
Kazalika, wasu ‘yan bindigar sun kashe wani babban limami saboda yawan sukarsu a hudubarsa.
Kimanin mutum 18 ake zargin mahara sun kashe tare da sace wasu matan aure biyu yayin wasu jerin hare-hare a ƙaramar hukumar Giwa dake jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa, Kwamishinan al’amurran cikin gida da sha’anin tsaro, Samuel Aruwa, ya ce farmakin ya faru ne a ƙauyukan Kaya dake da iyaka da Hayin Kaura ta jihar Katsina, kamar yadda TheCable ta rawaito.
Read Also:
A cewar Kwamishinan, an fara kai hare haren ne tun ranar juma’a lokacin da ake murnar shiga sabuwar shekara, ya kara da cewa cikin waɗanda maharan suka sace harda wata matar aure.
Da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin asabar ne kuma, wasu mahaya babura sama da su 50 ɗauke da mutum 3 tare da bindiga ƙirar AK-47, suka shiga ƙauyen na Kaya suka rinƙa harbi kan mai uwa da wabi.
“Rikicin ya faro tun 1 ga watan Janairun 2021 lokacin da maharan suka farwa ƙauyen Kaya, suka kashe tare da sace mutane garin ciki harda wata matar aure” in ji Samuel Aruwa.
Ya ƙara da cewa, “Maharan sun fuskanci mummunar turjiya daga yan sa kai na Kaya, da kuma wasu daga Hayin Kaura dake jahar Katsina a ƙoƙarinsu na inganta tsaro a yankunansu.”
Ya ce, an rasa rayuka da dama amma dai rundunar sojin Najeriya haɗin gwiwa da ta yan sanda, sun yi kokari wajen aike da dakaru cikin gaggawa yankin tare da jirgin sojin sama.