Wani Dan Najeriya Zai Samu Matsayi a Fadar Sabon Shugaban Amurka
Joe Biden zai tafi da wasu bakakaken fata idan ya hau kan karagar mulki.
Biden zai ba Adewale Adeyemo kujerar karamin Minista a gwamnatinsa.
Cecilia Rouse da Neera Tanden za su samu wuri idan Biden ya dare mulki.
Bayan makonni ana sukar nadin mukaman da Joe Biden zai yi, zababben shugaban na Amurka ya zabi wasu da ba ainihin Amurkawa ba a cikin gwamnatinsa.
Mista Joe Biden ya zabi wasu mutane uku da ba farare ba a cikin majalisar tattalin arzikinsa.
Kamar yadda wasu na kusa da Biden su ka bayyana, Cecilia Rouse ce za ta rike kujerar shugaban masu bada shawara a majalisar tattalin arzikin kasar Amurka.
Read Also:
Rouse mai shekara a 56 a Duniya, asalinta mutumiyar nahiyar Afrika ce da ta ke zaune kuma ta yi karatun ilmin tattallin arziki a jami’ar Princeton ta Amurka.
Mutane akalla biyu sun tabbatar da cewa Cecilia Rouse ta na da wuri a gwamnatin Joe Biden.
Jaridar Punch ta ce ana kishin-kishin Adewale Adeyemo wanda ya yi aiki da gwamnatin Barack Obama, zai rike kujerar mataimakin ministan asusun Amurka.
Adewale wanda aka fi sani da Wally haifaffen Najeriya ne, wanda ya rike kujerar mai bada shawara a kan harkar tattalin arzikin kasa tsakanin 2015 da 2016.
A kujerar kula da kasafin kudi, Neera Tanden ake yi wa hangen wanda za ta rike wannan ofis.
Neera Tanden mutumiyar Indiya ce wanda ta yi aiki da Barack Obama da sakatariyar gwamnati, Hillary Clinton. Tanden ita ce shugabar cibiyar American Progress.