‘Dan Najeriya ya Janyo Cecekuce Yayi da ya je Zuba $500,000 Wacce Tayi Daidai da N220m a Asusun Banki
Hoton ‘dan Najeriya wanda yaje zuba kudi har $500,000 wanda yayi daidai da N220 miliyan a banki, ya janyo maganganu a soshiyal midiya.
Mutumin da har yanzu ba a san sunansa ba, ya kwashi kudin zuwa banki bayan ya samu labarin kokarin CBN na sauya fasalin Naira.
Rade-radin da ake yadawa na cewa Amurka ba zata karba wasu takardun daloli ba ya matukar ruda jama’a dake da su a ajiye.
Wani mutum ‘dan Najeriya ya janyo cecekuce a wani banki da ya shiga inda ya je zuba $500,000 wacce tayi daidai da N220 miliyan a asusun banki.
Hoton mutumin da har yanzu ba a gano sunansa ba, ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani kuma jama’a suna ta yin Allah Amin kan wannan lamari.
Karantsare ga dokar kudade
Hoton an dauke shi ne a wani banki wanda ba a gano ba har yanzu kuma ya bar ‘yan Najeriya da maganganu kan dalilin da yasa wadannan makuden kudaden za a boye su ko kuma mutum ya adana su da kan shi.
Har yanzu dai babu tabbacin ko mutumin yayi karantsaye ga dokokin kudi na Najeriya kan boye dalilin da yayi wanda ya kawo lalacewar darajar Naira.
Read Also:
A makon da ya gabata, babban bankin Najeriya ya debo $1.8 biliyan daga ma’adanar Najeriya wanda hakan yasa ma’adanar tayi kasa.
Wani mutum yace:
“Kada ku yi hassada da shi. Ku ka san ko kidinafa ne, ‘dan ta’adda ko ‘dan bindiga? Su ne ke karbar kudin fansa a daloli yanzu.”
Wani yace:
“Ku cigaba da yin kamar baku san komai a kai ba. Kudin da kuka aika wani ya saka a daskararren asusun bankin ku kuma kuka bukaci ya dauka hoto ya turo muku shaida.”
Yawaitar daloli a kasuwa a cikin kwanakin nan yana daga cikin dalilin da yasa naira ke kara daraja.
Me masu kiyasi ke cewa?
Masu kiyasi sun yarda cewa da yawan wadanda suka boye daloli ko suke canza naira zuwa daloli suna cika kasuwanni da dalolin sakamakon bayanin Amurka.
Abbas Yishau, wani ‘dan jarida dake aiki da gidan rediyo a Kano, ya sanar da Legit.ng cewa da yawa daga cikin masu boye dalolin suna tsoron cewa wasu daga cikin kudin da suke dasu zasu tashi aiki.
Kamar yadda Yishau yace, rade-radin da ake fadi na cewa Amurka ta ja kunnen cewa wasu takardun kudin da aka buga kasa da 2021 ba za a dinga karbar su ba, hakan ne yasa aka cika kasuwa da dalolin.
Wani ‘dan kasuwar canji dake Legas, Ishaya Abdul, yace halin yanzu dalolin sun cika kasuwa.
Yace da yawa daga cikin ‘yan canji suna neman yadda zasu yi da dalolin da suka boye saboda jan kunnen Amurka.