Jami’in ‘Dan Sanda ya Harbe Abokin Aikinsa a Jahar Kano
Wasu jami’an ‘yan sanda sun samu sabani tsakaninsu, lamarin da ya kai daya ya harbe daya.
Rahoto ya bayyana cewa, jami’in ya harbe dan uwansa ne saboda yana masa dariya kawai.
Tuni aka mika shi ga cibiyar bincike da CID don gudanar da bincike ciki har da lafiyar kwakwalwarsa.
Kano – An harbe wani jami’in dan sanda mai suna Sufeto Ya’u Yakubu a hedkwatar ‘yan sanda na yankin Warawa da ke jahar Kano, Daily Trust ta rawaito.
An ce Sajan Basharu Alhassan ne, wani abokin aikinsa a sashen da suke ya harbe shi.
Read Also:
Yayin tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an garzaya da marigayin zuwa babban asibitin Wudil inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Kiyawa ya kara da cewa nan take aka cafke Sajan Basharu Alhassan.
Ya kara da cewa yanzu haka an tura wanda ya yi kisan zuwa CID na jahar, za a yi masa gwaji don tabbatar da lafiyar kwakwalwarsa kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jahar, CP Sama’ila Dikko ya ba da umarni.
A cewar Kiyawa:
“An samu rashin fahimtar juna ne tsakanin jami’an biyu kuma a sakamakon haka, Sufeto ya harbi Sajan din.”
“A bincikenmu na farko, sugeton ya ce bai ma san lokacin da ya harbe abokin aikin nasa ba kuma yana iya tuna cewa marigayin yana yi masa dariya. Don haka ya fita hayyacinsa kuma ya aikata wannan aikin.”
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jahar ya ba da umurnin a mika karar zuwa sashen binciken manyan laifuka na CID na jahar, domin ba su damar gudanar da bincike na gaskiya a kan lamarin.