ɗan Sandan da Ake Zargi da Harbe Yarinya a Kamaru ya Shiga Hannun Hukuma

Hukumomi sun kama ɗan sandan da ake zargi da harbe wata yarinya mai shekara takwas a Kamaru.

Ɗan sandan ya yi harbi kan wata mota da ta tsere wa wurin duba ababen hawa ranar Juma’a a birnin Bamenda da ke fama da tashin hankali na ‘yan tawaye.

Mutuwar yarinyar ta jawo zanga-zanga a yammacin Juma’a inda aka raunata aƙalla mutum biyu. Kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun rawaito cewa jami’an tsaro sun buɗe wa ‘yan zanga-zangar wuta.

Sai dai wani soja da ke wurin ya ce jami’an tsaron sun yi harbi a sama ne don tarwatsa mutanen.

Bamenda ne babban birnin ɗaya daga cikin biyu na yankunan rainon Ingila da ke fama da fafutikar tawaye, inda mayaƙan ke iƙirarin cewa gwamnatin ƙasar na zalintarsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here