Ɗan sanda ya Rasa Ransa a Harin da ‘Yan Boko Haram Suka Kai wa Tawagar Shugaban Karamar Hukuma a Borno
Wasu yan bindiga da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai wa jerin gwanon motoccin shugaban karamar hukumar Nganzai a Borno hari.
Mohammed Bashir Bukar, hadimin shugaban karamar hukumar Nganzai, Hon Asheikh Mamman ya ce mai gidansa lafiyarsa lau kuma ba a sace shi ba.
Bukar, amma ya ce jami’in dan sanda guda daya daga cikin tawagar ya riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da yan ta’addan suka kai musu a hanyar su ta zuwa wani aiki.
Borno- Ɗan sanda ya riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai wa tawagar motocin shugaban karamar hukumar Nganzai a Jihar Borno, Hon Asheikh Mamman Gadai, hari a ranar Laraba.
Read Also:
Lamarin ya faru ne a hanyar Gajiram da Gajiganna lokacin da Asheikh da tawagarsa ke hanyarsu ta zuwa wani aiki, rahoton Daily Trust.
Hadimin Asheikh ya tabbatar da afkuwar harin A cikin sanarwa, Mohammed Bashir Bukar, mataimaki na musamman ga shugaban karamar hukumar Nganzai a bangaren watsa labarai ya tabbatar da harin.
Sanarwar ta ce Hon Asheikh lafiyarsa kalau, ɗan sanda cikin tawagarsa ya rasu.
An bukaci al’umma su yi watsi da jita-jitar cewa yan ta’addan sun sace Hon Asheikh. Amma, sanarwar ba ta bada karin bayani game da harin ba.
An yi kokarin ji ta bakin Bukar a lokacin hada wannan rahoton amma ba a same shi ba.
A halin yanzu dai Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro da ake yi wa kallon mafi muni a tarihin kasar.
Dakaci karin bayani…