Akwai Yiyuwar Jihohi 16 su Fuskanci Yunwa da Karancin Abinci – ‘Yan Majalisa

 

Majalisar wakilan tarayya ta hango yiwuwar wasu Jihohi su auka cikin matsin yunwa nan gaba.

Kwamitin harkokin noma a majalisar tarayya sun bukaci a fara daukar matakin da ya kamata.

Hon. Rimamnde Shawulu ya gabatar da bayani a zauren majalisa, inda ya ankarar da hukumomi.

FCT, Abuja – Majalisar wakilan tarayya tace lamarin tabarbarewar tsaro da karancin kayan abinci yana kara yaduwa zuwa wasu jihohin da ke kasar nan.

Kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli 2022, majalisar tarayyar tace matsalar abinci za ta shafi akalla jihohi 16.

Majalisar tace abin da ya karo jawo matsalar tayi kamari shi ne yadda ‘yan bindiga suka labe a gonaki, suna yin awon gaba da manoma a wasu yankunan.

Miyagun ‘yan bindiga suna aukawa manoma, suna garkuwa da mutane a kauyuka da nufin samun kudi, tare da hana manoma zuwa gona sai sun biya kudi.

Wannan ta’adi da ‘yan bindigan ke yi ya taimaka wajen jawo manoma su gujewa gonakin na su.

Kiran kwamitin noma a Majalisa

Kwamitocin harkokin gona na majalisar wakilan Najeriya sun yi kira ga ma’aikata da hukumomi da kungiyoyin Duniya su dauki matakin magance matsalar.

Rahoton yace kwamitocin sun bukaci a fara dabbaka matakan da za su taimaka wajen magance matsalar karancin abinci a duka jihohin da abin ya shafa.

An cin ma wannan matsaya ne bayan sa bakin Honarabul Rimamnde Shawulu da Honarabul Solomon Bob.

Akaluman da suka fito daga CBN

Da yake gabatar da kudirinsa a zauren majalisar a ranar Laraba, Rimamnde Shawulu ya kafa hujja da wani rahoto na shigo da abinci da bankin CBN ya gabatar.

A cikin shekara daya, kudin kasar wajen da ake kashewa wajen shigo da kayan abinci Najeriya ya karu da 45%, an batar da Dala biliyan 2.71 a shekarar 2021.

Shawulu ya nuna cewa kasashen Duniya suna cikin wannan matsala na yiwuwar fama da yunwa wanda ake zargin yakin Rasha da Ukraine ya ta’azzara shi.

Akwai matsala – Hon. Mustapha Shehuri

Tun a shekarar bara aka ji Karamin ministan noma da raya karkara, Mustapha Shehuri, ya bayyana cewa Najeriya na iya fama da karancin kayan abinci.

A yanzu maganar da ake yi shi ne Majalisar dinkin duniya tace ana bukatar sama da Naira biliyan 150 kafin a ciyar da mutanen da ke zaune a Arewa maso gabas.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here