Tsohon Gwamnan Filato, Dariye ya Musanta Aniyar Tsayawa Takara a Zaben 2023

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa wasu da aka daure bisa sace kudin afuwa, ‘yan Najeriya sun fusata.

A makon nan ne aka samu rahotannin da ke cewa, tsohon gwamnan Filato Dariye zai tsaya takarar sanata.

A rahoton da muka samo yau Juma’a, tsohon gwamnan ya musanta aniyar tsayawa takara tare da yin karin haske.

Jihar Filato – Tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, wanda aka saka kwanan nan daga gidan yari watanni uku bayan da Buhari ya yi masa afuwa, ya ce ba zai wani tsaya takarar kujerar majalisar dattawa ta Filato ta tsakiya ba a zaben 2023 ba.

Dariye, wanda ke zaman gidan yari na shekaru 10 a gidan yari, ya shaki iskar ‘yanci a ranar Litinin din da ta gabata bayan kimanin shekaru hudu yana daure.

Tun bayan da aka sake shi ake ta ta rade-radin cewa tsohon gwamnan ya kammala shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour, domin karbar fom din takarar sanata domin wakiltar al’ummar yankin Filato ta tsakiya.

Sai dai da yake magana a wani taro, Dariye ya yi watsi da hakan, inda ya karya ajita-jitar aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata, kuma ya ce ba shi da niyyar tsayawa takarar a 2023 ko da wasa.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya jagoranci tawagar jihar da suka ziyarci Dariye da tsohon gwamnan jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame, domin taya su murna samun ‘yanci da kuma afuwar Buhari.

Batun gaskiya game da takarar Dariye

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Lalong, Macham Makut ya fitar a ranar Juma’a bayan ziyarar ta ce:

“Shi (Dariye) ya ba da labarin irin wahalar da ya sha a gidan yari, ya ce lokaci ne mai wahala amma Allah ya taimake shi kuma ya sa ya tsira.

“Dariye ya kuma karyata rade-radin da ake yadawa na cewa ya fito takarar Sanata, yana mai bayyana hakan a matsayin batu mara tushe kuma ba gaskiya ba ne domin bai sayi fom ba ko kuma ya yi wani abu mai kama da haka.”

Hakazalika, sanarwar ta bayyana cewa nan da mako mai zuwa ne Dariye zai je Jos domin gode wa magoya bayansa da masoya da suka tsaya masa a tsawon wadannan shekaru, kamar yadda Pulse ta ruwaito.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here