Kungiyar Dattawan Arewa ta yi Martani Kan Canza Shugabannin Tsaro da Shugaba Buhari ya yi

 

Kungiyar dattawan arewa (NGF) ta ce ba canja shugabannin tsaro kadai ne zai kawo karshen rashin tsaro ba a Najeriya.

Ta ce wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya tsayin-daka a matsayinsa na kwamandan shugabannin tsaron don bayar da umarni.

A cewar NGF, duk da an daina sanya bama-bamai a kasar nan yanzu, amma Boko Haram da masu garkuwa da mutane sun gama illata kasar nan.

NGF ta ce ba canza shugabannin tsaro ne kadai zai kawo garanbawul ba ga matsalolin tsaron da Najeriya take fuskanta, Punch ta wallafa hakan.

Wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya sanya ido kuma ya dinga bai wa shugabannin tsaro umarni yadda ya dace a matsayinsa na kwamandansu.

“Babban matakin da Buhari zai dauka shine canja salo da kuma fuskantar matsalolin tsaro gadan-gadan.

Sai ka ji yana cewa ya taras da tabarbarewar tsaron Najeriya a 2015 ya nunka halin da ake ciki yanzu, wannan kalaman suna matukar tayar da hankali.

“Tabbas an daina sanya bama-bamai a Najeriya, amma ‘yan Boko Haram sun riga sun kashe mutane masu yawa marasa adadi, ba za mu cigaba da lamuntar hakan ba,” Yace.

Kakakin NGF, Dr Hakeem Baba-Ahmed a ranar Laraba yayin da Channels ta ke tattaunawa dashi ya fadi hakan.

A cewarsa arewa maso gabas tana cikin wani hali wanda take bukatar dauki daga shugabannin tsaro.

A cewar Baba-Ahmed, ba nadin kadai ne zai kawo canji ba, ana fatan ya dauki matakin ne ba don surutun jama’a ba, sai don kawo karshen tashin hankali, rikici da rashin tsaro da kasarnan take fuskanta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here