Nan Gaba Kaɗan Za’a Fara ɗaukar ƙananan Jami’ai 20,000 – Hukumar ‘Yan Sanda

 

Hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewa ba da jimawa ba zata fara shirin ɗaukar sababbin kananan jami’ai 20,000.

Sufeta janar na yan sandan ƙasar nan, IGP Usman Baba, yace duk wasu matsaloli da suka sa jinkirin ɗaukar jami’an an ci ƙarfin su.

Gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde, yace ya zama wajibi a cigaba da nuna goyon baya ga jami’an yan sanda.

Ibadan, Oyo – Sufeta janar na rundunar yan sandan ƙasar nan, Usman Alkali Baba, yace nan gaba kaɗan za’a fara ɗaukar ƙananan jami’ai 20,000, kamar yadda Premium Times ta rawaito.

IGP ya yi wannan furuci ne ranar Talata da yamma, yayin da yakai ziyarar aiki ga gwamna Seyi Makinde na jahar Oyo, a Ibadan.

Baba ya shaidawa gwamnan cewa rundunar yan sanda ta shirya ƙara wa jami’anta ƙarfi ta hanyar ɗaukar sabbin kurata.

Ya ƙara da cewa hukumar yan sanda ta samu nasarar warware duk wasu matsaloli da suka sa jinkirin ɗaukar sabbin jami’an, kuma tuni shugaba Buhari ya amince da shirin.

Kowane yanki zai amfana

Sufetan yan sandan yace kowace ƙaramar hukuma zata amfana da sabbin kananan jami’ai da za’a ɗauka.

Kowane mutum da aka ɗauka zai yi aiki ne a ƙaramar hukumarsa da yake zaune, a cewar IGP Usman Baba.

Bugu da ƙari, IGP yace shirin ɗaukar jami’an yana da alfanu sosai kuma zai taimaka wa tsarin tsaro na kowane yanki.

Menene maƙasudin ziyarar IGP?

Sufetan yan sandan yace ya kawo wannan ziyarar aikin ne domin ganawa da jami’an yan sanda da kuma kara musu karfin guiwa bayan zanga-zangar EndSARS.

Ya kuma bukaci gwamnan jahar da ya cigaba da goyon bayan jami’an yan sanda da kuma tallafa musu a aikin su.

Yan sanda suna kokari – Gwamna Makinde Da yake nasa jawabin, Gwamnan Oyo, Makinde, ya bayyana cews jami’an yan sandan jahar na yin iyakar bakin kokarinsu, haɗa kai da mutane da sauran hukumomin tsaro.

Gwamnan yace:

“Mun san cewa wannan lokaci ne mai matukar wahala da ƙalubale a ƙasar nan, babu isassun kuɗaɗe kuma ga tarin matsaloli.”

“Saboda haka ya zama wajibi a gare mu, mu cigaba da goyon bayan namijin kokarin da rundunar yan saɓda take yi.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here