Yadda DCP Abba Kyari ya ‘Tatsi’ N41m Daga Hannun Yani Dan Kasuwa

Afeez Mojeed, wani ɗan kasuwa mazaunin Legas ya yi ikirarin fittacen ɗan sanda, DCP, Abba Kyari da jami’ansa sun amshe masa N41m.

Mojeed ya bayyana hakan ne cikin wata takardar ƙorafi da ya gabatar wa kwamitin binciken wadanda jami’an SARS suka zalunta a Legas – Mojeed ya yi iƙirarin wannan lamarin ya faru ne a shekarar 2014 a lokacin Abba Kyari na shugabancin rundunar SARs a Legas Wani ɗan kasuwa mazaunin Legas mai suna Afeez Mojeed ya bayyana cewa mataimakin kwamishinan ƴan sanda, DCP, Abba Kyari ya tatsi naira miliyan 41 daga hannunsa.

Mojeed ya yi iƙirarin cewa wannan lamarin ya faru ne a shekarar 2014 lokacin Kyari shugaban tsohuwar rundunar SARS a Legas kamar yadda The Cable ta ruwaito. A shekarun 2016 da 2018, Mojeed ya nemi a ƙwato masa hakkinsa ta hanyar shigar da ƙorafi a hukumar Yaki da rashawa, ICPC da NHRC amma bai yi nasara ba.

A sabuwar ƙorafin da ya shigar a ranar 22 ga watan Oktoba ta hannun lauyansa Salawu Akingbolu & Co ga kwamitin da aka kafa don sauraron ƙorafin wadanda SARs suka zalunta a Legas, Mojeed ya zargi Kyari da jami’ansa da ƙwatar kayyaki 32 daga gidansa a 2014. Gwamnatin Jihar Legas ta kafa kwamitin sharia don sauraron korafin mutane musamman wadanda tsaffin jami’an SARS suka zalunta bayan zanga zangar rushe rundunar.

A ƙorafin da ya shigar, Mojeed ya ce ya faɗa tasku ne a daren ranar 18 ga watan Oktoban 2014 inda wasu jami’an SARS hudu suka afka gidansa dauke da bindigu. Ɗan kasuwan ya ce yana gida tare da matarsa mai juna biyu, ɗan su da surukarsa a lokacin da suka afka masa tamkar ƴan fashi. “Sun ƙwace zoben aurensa da na matarsa, suka kwace N280,000 daga cikin gidansa kuma suka dauki N50,000 daga motarsa Honda Accord (2008) wacce suka tafi da ita,” a cewar takardar korafin.

An kuma karbe wayoyi, takardun cire kudi a banki, katin ATM da wasu takardu masu muhimmanci a gidan. Kwana 14 a tsare Bayan bincike gidansa an kai Mojeed ofishin SARS da ke Ikeja inda aka tsare shi na kwanaki 14 daga 18 ga watan Oktoba zuwa 31 ga watan Oktoba na 2014. Daga baya an gurfanar da shi kan zargin aikata laifin sata na Naira miliyan 97 amma kuma ƴan sandan ba su hallarci zaman kotu ba hakan yasa daga bisani kotu ta ta yi watsi da Kara.

A cewar takardar ƙarar, yayin da ya ke tsare “ƴan sanda ƙarƙashin jagorancin Abba Kyari (OC SARS) sun tilasta masa saka hannu kan takardar bankinsa ya fitar da N450,000 a ranakun 22 – 23 ga watan Oktoban 2014 ya mika wa wani Olawale Nuruddeen ɗaya daga cikin abokinsu don ya ciro kuɗin.” Ya kuma yi iƙirarin cewa ƴan sandan sun karbi lambar sirri na bakinsa sun cira kuɗi N395,000 daga asusunsa daga ranar 20 zuwa 23 ga watan Oktoban 2014.

Ƙwatar Naira miliyan 41

Har wa yau, takardar ƙorafin ta ce ƙarƙashin jagorancin Abba Kyari an kai “Mojeed banki an tilasta masa tura Naira miliyan 41 da N800,000 zuwa asusun wani da ake zargin sun raba da ƴan sandan ne.” Lauyan Mojeed ya ce ya gana Abba Kyari a ofishinsa da ke Legas a wancan lokacin amma ya faɗa masa cewa ya ajiye kuɗin a matsayin shaida ne. “Sai dai har zuwa yanzu ba dawo masa da kuɗin ba kuma sun samu rahoton Abba Kyari ya tafi da motar,” a cewar takardar korafin.

An kuma yi zargin cewa Kyari ya nemi hada baki da lauyan Mojeed don su damfare shi. Babban ɗan sandan ya fadawa lauyan cewa Mojeed ɗan damfarar intanet hakan yasa ya karbe kuɗin daga hannunsa. An yi wa lauyan barazana idan bai bada hadin kai ba a cewar rahoton. Rahoton likita mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Nuwamba 2014 da majiyar Legit.ng ta gani ya nuna cewa Mojeed ya yi fama da ciwon kunne, ido da ƙirji bayan cin zalinsa da ƴan sanda suka yi. A lokacin rubuta wannan rahoton, Kyari, wanda a yanzu shi ke jagorantar rundunar ta musamman na IRT bai yi tsokaci kan batun ba don wayoyinsa na kashe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here