Gwamnan Jahar Delta ya Sallami kwamishinoninsa 25, Shugaban Ma’aikata da Sakataran Gwamnatin Jahar
Gwamnan jahar Delta ya sallami kwamishinoninsa 25, sakataren gwamnatinsa da kuma shugaban ma’aikatan fadarsa.
Kamar yadda tsohon kwamishina yada labarai na jahar ya sanar, yace gwamnan yayi haka ne domin baiwa sabbin jini damar taka rawarsu a mulki.
Sai dai an sallami Bernard Onomovo ne sakamakon kama shi da aka yi da laifin saka wasu sunayen bogi cikin masu karbar albashin gwamnatin jahar.
Gwamna Ifeanyi Okowa na jahar Delta a ranar Talata ya sallami kwamishinoni 25, sakataren gwamnatinsa, shugaban ma’aikatan fadarsa, babban mai bashi shawara a harkar siyasa da sauransu.
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, tsohon kwamishinan yada labarai na jahar, Charles Aniagwu, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jihar, ya ce wannan al’amarin an yi shi ne domin baiwa sabbin jini damar taka rawarsu.
Read Also:
Aniagwu ya bayyana wadanda lamarin ya shafa sun hada da kwamishinoni 25, sakataren gwamnatin jahar, Chiedu Ebie, shugaban ma’aikatansa, David Edevbir, babban mai bada shawara kan siyasa, Funkekeme Solomon, tare da wasu masu bada shawara na musamman.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Gwamna Okowa ya mika godiyarsa ga dukkansu sakamakon rawar da suka taka a gwamnatinsa na tsawon shekaru shida inda yace sun bada gudumawa wurin samar da cigaba a jahar.
Majalisar zartarwar jahar ta amince da sallamar Bernard Onomovo sakamakon kama shi da aka yi da laifin zuba wasu sunayen bogi a cikin wadanda ake biya albashi a jahar.
Aniagwu ya ce Bernard ya kalubalanci hukuncin inda ya nuna cewa bashi da laifi ko kadan. Ya ce: ”
‘Yan majalisa sun amince da sallamar Bernard Onomovo wanda ke da hannu wurin saka wasu sunaye a cikin masu albashin jahar.
“Kusan shekaru biyu da suka gabata, an bukaci yayi murabus bayan an bincike shi amma sai yayi karar ‘yan majalisar zartarwan inda aka sake bincike aka gano ya aikata laifin.
“An sallameshi ne saboda ya bata lokacin ‘yan majalisar kuma ya cigaba da karbar albashi har na tsawon shekaru biyu.”