Direbobin Motocci Haya na Jahar Legas Sun Shiga Zanga-Zanga

Fasinjoji na shan wahala sakamakon zanga-zangar direbobin motocci ke yi a Jahar Lagos.

Direbobin sun tsunduma zanga-zangar ne saboda wasu kudade da hukumar harajin Jahar Lagos ta kakaba musu.

Wasu direbobin na dauke da makamai kuma suna farmakar duk wanda ya yi yunkurin daukar fasinja.

Direbobin motoccin haya a Lagos a ranar Laraba sun shiga wata zanga-zanga sakamakon wani kudi da hukumar tara kudin shiga ta Jahar Lagos ta kakaba musu biya, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Zanga-zangar ta janyo cikowar fasinjoji daga Agege-Ogba-Berger na garin Lagos, ta kuma jefa fasinjoji cikin wahala inda wasu da dama cikinsu suka rika taka wa da kafafunsu zuwa wuraren da za su tafi.

Zuwa karfe 12:14 na rana, lamarin tuni yayi kamarin da ya janyo wa fasinjoji tattaki mai nisa.

Wasu daga cikin direbobin sun rike makamai don tunkarar masu kame.

Suna kuma kaiwa duk wani direba da ya yi yunkurin daukar fasinja hari.

Masu zanga-zangar sun rufe titin da ke sanannen mahadar Omole.

Kawo yanzu hukumar harajin ta jahar Legas bata bada ba’asi kan lamarin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here