Ɗiyar Solomon Ewuga Ta Mutu Tare da Mutane 11 Sanadiyyar Hatsarin Jirgi

Ɗiyar tsohon ministan Abuja kuma jigo a PDP, Solomon Ewuga, da ke aikin tuƙin jirgin sama ta mutu tare da wasu mutum 11 a haɗarin jirgi.

Bayanai sun nuna cewa Adzuayi Ewuga, ta rasa rayuwarta ne bayan karamin jirgin ya rasa sadarwa da Filin jirgi.

Jirgin ya yi hatsari ne a kudancin babban birnin ƙasar Kamaru bayan ya taso daga filin sauka da tashin jirage na Yaounde Nsimalen.

Matuƙiyar jirgin sama yar Najeriya, Adzuayi Ewuga, ta rasa rayuwarta a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da ita a tsakiyar ƙasar Kamaru, kamar yadda Leadership ta rawaito.

Marigayyar ɗiya ce ga Sanata Solomon Ewuga, wani jigo a jam’iyyar hamayya PDP a jihar Nasarawa kuma tsohon ƙaramin ministan babban birnin tarayya, Abuja.

Matuƙiyar jirgin ta mutu ne tare da wasu mutum 11 a wani ƙaramin jirgi mallakin Ma’aikatar kula da harkokin sufurin jiragen sama na Kamaru, wanda ya yi hatsari sanadiyyar katsewar sadarwa.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya taso ne daga filin jirgin Yaounde Nsimalen ya nufi Belabo da ke gabashin ƙasar ƙasar, lokacin da haɗarin ya auku, duk na ciki suka mutu.

Ma’aikatar kula da harkokin sufurin jirgi ta Kamaru na da alaƙa da Caverton Offshore Support Group, da ke Legas a Najeriya, kuma sukan taimaka wa jiragen Kamaru, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Legit.ng ta tattaro cewa wannan shi ne babban haɗarin jirgi na farko da ya auku a Kamaru tun bayan abin da ya farua shekarar 2007.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here