Alherin da na Shirya Yiwa ‘Yan Najeriya Idan na Zama Shugaban Kasa – Saraki

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya bayyana alherin da ya shirya yiwa ‘yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

Saraki ya ce idan aka zabe shi zai tabbatar da gina gidaje 500,000 duk shekara ga ‘yan Najeriya a mulkinsa.

Ya kuma bayyana cewa, zai zama mai hada kan ‘yan Najeriya; Kudu da Arewa, Musulmi da Kirista baki daya.

Abuja- A ranar Alhamis ne tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya yi alkawarin gina gidaje 500,000 a duk shekara idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasan Najeriya a zaben 2023.

Saraki wanda ke tseren takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP ya kuma yi alkawarin zai zama gada tsakanin Arewa da Kudu da Kirista da Musulmi, jaridar Punch ta rawaito.

Saraki ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja.

“Zan gina gidaje 500,000 masu araha duk shekara. Zan kirkiro dandali mai inganci don kare nahiyar Afirka. Zan zama shugaban kasa ga kowa da kowa saboda zan wakilci Najeriya ne. Zan zama gada tsakanin Arewa da Kudu, Musulmi da Kirista.”

Hakazalika, Bukola Saraki, ya ce zai kare kowane bangare na kasar nan daga ‘yan ta’adda da ‘yan fashi idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Ya ce dogaro da man fetur da al’ummar kasar ke yi zai zo karshe a mulkinsa saboda bangaren da ba na mai ba zai fi kawo ci gaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here