‘Iyaye Sun Maka Ɗansu a Gaban Kotu Kan Kin Haihuwa

 

Ma’auratan wadanda yan asalin kasar Indiya ne, sunce dan nasu ya yi aure tsawon shekaru shida amma har yanzu baya tunanin haihuwa tare da matarsa.

Rokon da suke yi a kotu shine cewa imma dan ya biya su $650,000 (N270m) a matsayin diyya ko kuma ya haifa masu jika cikin shekara daya.

Indiya – Wasu ma’aurata yan kasar Indiya masu suna Sanjeev da Sadhana Prasad sun maka dansu a kotu kan kin haifa masu jika, duk da ya shafe tsawon shekaru 6 da aure.

Ma’auratan wadanda ke cike da bakin ciki suna so ya saka masu domin sun kashe abun da suka tara a wajen tarbiyantar da shi da kuma basa ilimi.

Ma’auratan sun ba dan nasu zabi biyu

A karar da suka shigar a makon da ya gabata, The Times Indiya ta rahoto a ranar Alhamis cewa ma’auratan sun bukaci dansu da gimbiyarsa su biya $650,000 wato N270m ko su haifa masu jika cikin shekara daya.

“Danmu ya yi aure tsawon shekaru shida amma har yanzu basa tunanin haihuwa. Akalla idan muna da jikan da za mu dunga zama tare, radadin da ke ranmu zai ragu,” cewar ma’auratan a karar da suka shigar kotu a Haridwar, Indiya.”

Ga rabe-raben kudin da Sanjeev da Sadhana Prasad suke so a biya su

Daily Star ta rahoto cewa ma’auratan da suka dauki bashi don gina gidansu suna fuskantar kalubale don haka suke so a basu toshiyar baki.

Suna so ya biya $80,000 (miliyan N33.2) da suka yi amfani da shi wajen siyawa dan nasu da matarsa motar alfarma.

Suna kuma so a biya su kudin da suka kashe wajen tura dan nasu cin angwanci a kasar waje da kuma na shagalin biki da aka yi a katafaren otel.

Iyayen sun kashe $65, 000 (miliyan N27) wajen horar da dan a matsayin matukin jirgin sama a kasar Turai, Gulf News ta rahoto. Sai dai ya dawo kasarsa Indiya ba tare da aiki ba.

A cewar lauyan ma’auratan Arvind Kumar, kotu za ta saurari karar da suka shigar a arewacin Indiya a ranar 17 ga watan Mayu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here