Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Karrama Shugaban Hukumar NITDA Malam Kashifu Inuwa da Lambar Yabo

 

A wani mataki na yabawa da ƙwazo, juriya, aiki tuƙuru, gami da ƙoƙarinsa na ciyar da Nageriya gaba kan harkokin fasahar zamani

Mai girma shugaban ƙasa, Malam Muhammadu Buhari, (GCFR), a yau, ya karrama mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, (CCIE) da lambar yabo ta jinjina da yabawa da irin ɗumbin nasarorin da ya samar, “National Productivity Order of Merit Award” (NPOM).

Bikin ba da lambar yabon ya gudana ne a Abuja fadar shugaban ƙasa, inda shugaba Buharin ya karrama Malam Kashifu Inuwan shi da hukumar da ya ke jagoranta ta (NITDA), tare kuma da wasu muhimman mutanen jimillar mutum (48) daga hukumomin gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu bisa abubuwan cigaba da su ma su ka samarwa ƙasar a fannonin ayyukan nasu.

Daga cikin muhimman mutanen da shugaba Buharin ya karrama yau sun haɗa da: sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha Gida, da kwamishinan lafiya na Jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi, da shugaban kamfanin jigilar jiragen sama na (Airpeace Airlines), Mista Allen Onyema, da kuma shugaban kamfanin samar da kayayyakin masarufi a Nageriya, (BUA), Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u, haɗi da shugaban Bankin Zenith, Mista Jim Ovia.

Sai kuma shugaban jam’iyyar (APC) na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da shugaban hukumar shawo kan cututtuka masu yaɗuwa, “Nigeria Centre for Disease Control” (NCDC) wanda ya sauka kwanan nan, Dakta Chike Ihekweazu, da shugaban (Globacom), Mista Mike Adenuga, da shugaban ƙungiyar lafiya ta yammacin Afrika, Farfesa Stanley Okolo. Dss.

Wannan gagarumin bikin ba da lambobin yabo ga muhimman mutane da su ka samarwa Nageriya wani abu na cigaba, shi ne karo na (19) da aka gabatar a wannan rana ta samar da abubuwa ta ƙasa, (National Productivity Day).

A jawabin da ya gabatar a wurin taron, ministan ƙwadago da samar da ayyuka na ƙasa, Mista Chris Ngige, ya labarta cewa tun bayan lokacin da aka yi irin wannan biki a shekarar (1991), gwamnatin Nageriya ta karrama ɗaiɗaikun mutane jimilla (382) da wannan lambar yabo ta (NPOM) da kuma ƙungiyoyi jimilla guda (97).

A jawabin da ya gabatar jim kaɗan da karɓar tasa lambar yabon, mai girma shugaban hukumar ta (NITDA), Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, (CCIE), ya bayyana farin cikinsa da godiya ga shugaba Muhammadu Buharin bisa wannan dama da ya ba su ta jan ragamar hukumar, gami da wannan lambar yabo babba, inda kuma ya ƙara da bayyana cewa lambar yabon za ta zama tamkar wani ƙarin ƙaimi a gare su wajen cigaba da bunƙasa tattalin arziƙi na fasahar zamani tayadda ƙasar za ta cigaba.

“Mu na godiya ta musamman ga mai girma shugaban ƙasa wanda salon shugabancinsa nagari abin koyi shi ya taimaka mana wajen samun wannan nasara”. Cewar Malam Kashifu.

Haka zalika kuma, ya ƙara da bayyana jinjina da yabo ga mai girma ministan sadarwa da tattalin arziƙin fasahar zamani, Shaik, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), dangane da kykkyawar shimfiɗar da ya yi wa hukumar a lokacinsa wanda hakan shi ne sirrin duk wata nasara da su ke samu kan tafikar da hukumar.

“Yabo ga mai girma minista, Farfesa Isah Ali Pantami bisa kykkyawan tubalin gini da ya ɗora a hukumar. Mu na godiya bisa jagoranci, haɗin kai da goyon baya gami da nusarwarsa”. Inji mai girma shugaban hukumar ta (NITDA), Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, (CCIE, NPOM).

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here