Doguwa/Tudun Wada: Hukumar INEC ta Bai wa Alhassan Doguwa Shaidar Sake Cin Zaɓe a Matsayin ɗan Majalisar Wakilai
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta bai wa Hon. Alhassan Ado Doguwa shaidar sake cin zaɓe a matsayin ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Doguwa da Tudun Wada, daga Jihar Kano.
Read Also:
Karo na shida kenan, da Ɗan Majalisar na tarayya ke samun nasarar zuwa majalisar ta wakilai daga Jihar Kano, da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya, tun bayan dawowar mulkin dimokraɗiyya a Najeriyar a cikin shekarar 1999.
Tun da farko dai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙara (INEC) ta soke nasarar Da Hon. Alhassan Ado Doguwa ya samu, a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, saboda jami’in sanar da sakamakon, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya ce “tursasa masa” aka yi.
Sai dai, jami’in sanar da sakamakon a zaɓen cike-giɓi na mazaɓar, Farfesa Sani Ibrahim a ranar 15 ga watan Afrilu, ya bayyana Alhassan Doguwa Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’u 41,572 bayan wannan zaɓen lafiya.