Majalisar Dattawa ta Saka Sabuwar Doka Akan Masu Biyan Masu Garkuwa da Mutane Kudin Fansa
Majalisar dattawa a ranar Laraba ta gabatar da sabuwar dokar haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa.
Ezrel Tabiowo, hadimin shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, a jawabin da ya saki ranar Laraba ya ce sabuwar dokar ta ketare mataki na biyu.
Ya kara da cewa Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ne ya gabatar da kudirin.
Dan majalisan ya bukaci a gyara dokar dakile ta’addanci an 2013 domin haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa don sakin wanda suka sace.
Read Also:
A cewar Onyewuchi, ya kamata a daure duk wanda ya biya masu garkuwa da mutane kudin fansa tsawon shekaru 15 a gidan gyara hali.
Sabuwar dokar itace: “Duk wanda ya tura kudi, ko ya biya kudi, ko ya tattauna da masu garkuwa da mutane don sakin wani ya aikata laifi kuma za’a iya dauresa a kurkuku na tsawon shekaru 15.”
Ya bayyana cewa dalilin haka shine garkuwa da mutane ya zama wani babban kasuwanci yanzu a Najeriya.
Ya bayyana cewa kasashe irinsu Amurka da Birtaniya basu yarda da biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa ba.
“Biyan yan ta’adda kudin fansa haramun ne karkashin dokar Birtaniya 2000 yayinda Amurka ta yanke bata yarda da biyan kudin fansa ba,” Onyewuchi ya kara.