Gwamnatin Jahar Jigawa ta Saka Dokar Hana Amfani da Babura Daga Karfe 9 na Dare Zuwa 6 na Safe

 

Jahar Jigawa ta sanya sabuwar doka ta hana hawa babura a fadin jahar domin magance rashin tsaro.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin jahar ta zauna zaman tattaunawa da kwamiin tsaron jahar.

An bukaci ‘yan jahar su bi wannar doka, sannan su tabbatar sun ba jami’an tsaro hadin kai wajen tabbatar da dokar

Jigawa – Gwamnatin Jigawa ta sanar da sanya dokar hana amfani da babura daga karfe 9 na dare zuwa karfe shida na safe a fadin jahar da nufin dakile karuwar rashin tsaro a sassan jahar, Channels Tv ta rawaito.

Shugaban karamar hukumar Dutse kuma shugaban ALGON a jahar, Alhaji Bala Usman Chamo, ya bayyana cewa an yanke wannan shawarar ne a taron majalisar tsaro na jahar wanda Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jahar ya jagoranta.

Tribune Nigeria ta rawaito cewa, Alhaji Bala Usman ya bayyana cewa “wannan wani bangare ne na matakan duba ayyukan masu aikata laifuka.”

A cewarsa:

“Haramcin wani bangare ne a kokarin gwamnati na dakile ‘yan ta’adda, ta amfani da babura wajen aikata laifuka, musamman a yankunan karkara na jahar.”

Dalilan da suka jawo sanya dokar Ya bayyana cewa an dauki matakin ne bayan Kwamitin Tsaro na jahar ya lura da karuwar barazanar tsaro a jahar.

Shugaban ALGON ya ci gaba da cewa:

“An lura cewa tsaro yana kara tabarbarewa a cikin kasar da jahar a matakin karamar hukumar mu. Mun samu faruwar matsalolin tsaro da dama a fadin jahar.

“Kuma wannan shine abin da ya haifar da shawarar kwamitin tsaro na sanya wasu matakai don sarrafa duk wani abin da zai iya haifar da karuwar matsalolin tsaro.

“Kuma matakin da aka dauka shi ne hana amfani da yawon babura daga karfe 9 na dare zuwa karfe 6 na safe, har sai an kara fitar da wata sanarwa.Duk wannan ya shafi dukkan kananan hukumomi 27 na jahar.”

An sanar da wadanda abin ya shafa

Shugaban ya kara da cewa an sanar da jagororin ‘yan achaba game da ci gaban don isarwa ga membobin su.

Ya kara da cewa, an kuma aika da sako ga dukkan hukumomin tsaro don tabbatar da aiwatar da umarnin kamar yadda kwamitin tsaro ya bayar da umarni.

Usman ya kara da cewa:

“Yana da mahimmanci a lura cewa duk wanda aka samu ya saba wa umarnin za a yi hukunta shi.

“Duk da haka, za a kebe wasu inda aka samu dalili mai ma’ana.”

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here