Dokar Haramta Achaɓa ta Fara Aiki a Kananan Hukumomi 6 da ke Birnin Legas
A wannan rana ta Laraba 1 ga watan Yuni, dokar haramta achaɓa da Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya kafa ta soma aiki a jihar Legas.
Haramcin achaɓa ya shafi kananan hukumomi shida da ke cikin birnin Legas, da suka haɗa da Ikeja da Lagos Island, Eti-osa da Apapa da Surulere da kuma Lagos Mainland.
Read Also:
Gwamna Sanwo-Olu ya umarci cewa daga 1 ga watan Yuni, jami’an tsaro a Legas su tabbatar da cewa an bi wannan doka da kuma maganin duk waɗanda suka karya doka.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas ta sake jaddadawa ‘yan jihar cewa duk mutumin da aka samu da karya dokar sai fuskanci hukunci mai tsauri.
A madadin hawa babur gwamnati ta sayo kananan jiragen ruwa da tace za a maye gurbin babura da su.
Wannan doka dai ta yi ta haifar da ce-ce-ku-ce tun lokacin da gwamnan ya sanar da matsayar sa a wani kokarin na sake tsaftace jihar da karin tsaro.