Dokar Kulle: Babu wata Sabuwar Doka – Lai Mohammed

Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta yi fashin baki kan jawabin kwamitin yaki da cutar Korona na ranar Litinin cewa an sake kakaba dokar kulle na tsawon makonni biyar sakamakon dawowan cutar.

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa babu sabon dokar kulle, kawai wasu matakai aka dauka dommin hana yaduwar cutar.

Ya bayyana hakan a hirar da yayi da Radio Nigeria.

Ministan ya ce sanarwar da kwamitin yaki da Korona PTF tayi a ranar Litnin, bai hada da dokar kulle ba kamar yadda wasu gidajen jaridar suka wallafa ba.

Ya kwantar da hankulan mutanen da suka kira waya a shirin domin jin gaskiyar lamarin saboda irin illan da sabuwar dokar kulle za tayi wa tattalin arzikin kasar.

Lai Mohammed ya yi bayanin cewa abinda gwamnatin tarayya tayi shine rage yiwuwan taruwar jama’a a waje guda.

“Gwamnati bata bada umurnin sabuwar kulle ba,” Lai yace. “Abinda muka yi shine mun sake dawo da tsaffin dokoki kuma mun umurci ma’aikatan gwamnatin tarayya masu mataki na 12 zuwa kasa su kasance a gida kuma zasu samu albashinsu.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here