A Saka Dokar ta Bace a Arewacin Najeriya Baki ɗaya – Gwamna Matawalle
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira da a saka dokar ta bace a arewacin Najeriya baki ɗaya.
Gwamnan yace yana da yakinin idan aka ɗauki wannan matakin za’a shawo ƙan matsalar tsaron da ta addabi yankin.
Arewacin Najeriya na fama matsalolin Boko Haram, ISWAP da kuma ayyukan ‘yan bindiga.
Zamfara – Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira a saka dokar ta baci a yankin arewacin kasar nan kan kalubalen tsaron da yaki ci yaki cinyewa, kamar yadda channels tv ta rawaito.
Gwamanan ya yi wannan kiran ne a gidan gwamnatin jahar dake Gusau, yayin gana wa da mataimakin sufeto janar na yan sandan kasar nan, Ali Janga, ranar Laraba.
Read Also:
Gwamnan ya nuna matukar damuwarsa kan jerin hare-haren da ake cigaba da kaiwa mafiyawancin jahohin yankin arewa maso yamma.
Bugu da kari matawalle yace yana da yakinin saka dokar ta ɓaci zai kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi arewa.
Arewacin Najeriya ya kunshi yankunan arewa maso gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya kuma ya kunshi jahohi 19 da babban birnin tarayya Abuja.
Menene babbar matsalar yankin?
Shekaru da dama da suka shuɗe, wasu sassa na arewa na fama da aikata manyan laifuka da suka haɗa da satar mutane, tada bama-bamai, da kuma kai hari kauyuka da garuruwa.
Zuwa yanzun, ɗaruruwan dubbanin mutane sun rasa rayukansu a yankin yayin da wasu miliyoyi aka tilasta musu barin mahallansu.
Boko Haram da ISWAP sune manyan kungiyoyin dake da alhakin hare-haren dake faruwa a yankin arewa maso gabas, kamar yadda Tribune Online ta rawaito.