Kylian Mbappa: Shin Ko PSG ta Yarda da Tayin Real Madrid Kan $188 ?

 

PSG ta yi watsi da tayin Real Madrid na dala miliyan $188m don ɗaukar ɗan wasa Kylian Mbappe.

Daraktan wasanni na PSG yace kungiyar ba zata siyar da ɗan wasa a wannan kuɗin ba.

Harry Kane na Tottenham ya bayyana cewa bai shirya barin kungiyar da yayi wayo a cikinta ba.

Madrid, Spain – Kungiyar PSG ta kasar Faransa ta yi fatali da tayin Real Madrid a kokarinta na ɗaukar ɗan wasan gaba, Kylian Mbappe ranar Laraba, kamar yadda punch ta rawaito.

Daraktan wasanni na PSG, Leonardo, yace tayin Real na kimanin $188 million “Yayi kaɗan” a kan ɗan wasan da suke son “Ya zauna a PSG.”

Ya kuma bayyana tayin da Real Madrid ta yiwa ɗan wasan wanda ya lashe kofin duniya da kasarsa ta Faransa a matasyin “Cin mutunci, bai dace ba kuma ya saba wa doka.”

Leonardo ya kara da cewa idan ɗan wasan mai shekara 22 yana son barin kungiyar babu wanda zai rikesa, amma “zai tafi ne ko ya zauna a kan sharuddan mu.”

Nawa PSG ta sayi Mbappe daga Monaco?

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa PSG ta lalewa Monaco zunzurutun kudi Yuro miliyan 180 domin raba ta da ɗan wasan a 2017, kuma a shirye take ta sabunta zamansa.

Tun bayan komawar Messi PSG, shugaban ƙungiyar, Nasser Al-Khelaifi, yace Mbappe ba shi da wani zaɓi illa ya zauna a PSG.

Zan cigaba da zama a Tottenham – Kane

Ɗan wasa gaba na kungiyar Tottenham ta kasar Ingila ya kawo karshen raɗe-raɗin tafiyarsa Man City ranar Laraba.

Kane, ɗan kimanin shekara 28, ya bayyana cewa yana nan daram a kungiyarsa ta Tottenham, kamar yadda channels tv ta rawaito.

Ɗan wasan gaban ya bayyana a fili cewa ba shi da kudirin barin kungiyar da ya taso tun yana karamin yaro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here