Ayyana Dokar Ta-ɓacin a Rivers Abin Damuwa ne kan Makomar Jihar – Gwamnan Bauchi

Gwamnonin jam’iyyar PDP sun buƙaci Shugaban Najeriya Bola Tinubu da ya janye dakatarwar da ya yi wa gwamnan Rivers Siminalayi Fubara.

Ƙungiyar Gwamnonin ta PDP ta bayyana dakatarwar da aka yi wa Fubara a matsayin “babban kuskure” sannan mummunan mataki ne da zai haifar da koma-baya.”

A ranar Talata da daddare ne Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan jihar Rivers sakamakon ƙiƙi-ƙaƙar siyasa da aka daɗe ana gani a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Shugaban ya kuma dakatar da Fubara da mataimakinsa da ƴanmajalisar dokokin jihar tare kuma da naɗa Ibok-Ete Ibas, tsohon soji mai muƙamin vice-admiral, a matsayin wanda zai ja ragamar al’amuran jihar.

Cikin wata sanarwa ranar Laraba, Bala Mohammed wanda shi ne gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya ce ayyana dokar ta-ɓacin a Rivers abin damuwa ne kan makomar jihar.

Gwamna Bala Muhammad ya ce jan baki ya yi shiru da Tinubu ya yi kan rawar da Nyesom Wike, ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja ke takawa a rikicin siyasar na Rivers kamar ba shi dama ce ya yi kiɗinsa kuma ya yi rawarsa.

Ya ce “Wike ya zama doka saboda yana yin abin da kake so. Yanzu mun sani. Wannan sam babu dattako, an nuna son kai da kuma rarraba kawuna,” in ji sanarwar.

Kungiyar gwamnonin ta PDP ta ce matakin ƙarara barazana ce ga dimokraɗiyyar Najeriya sannan zai ƙara rura wutar rikici a ƙasar tare da ƙara janyo rashin yarda da lalata tattalin arziki da kuma zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here