Abinda ya Zama Dole APC Tayi Don Samun Damar Zarcewa 2023 – Fashola

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce APC za ta cigaba da mulki a 2023, matsawar sun cika alkawuransu.

Ya ce wajibi ne ‘yan siyasa su dage wurin cika alkawuran da suka daukar wa al’umma don hakan ne abinda ya kamata.

A cewarsa, nasara tana harararsu, saboda gwamnonin jihohin da a baya suke adawa da su, yanzu sun fara komawa APC Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce jam’iyyar APC.

za ta cigaba da mulki a 2023, matsawar ta cika wa ‘yan Najeriya alkawuran da ta daukar musu.

Fashola ya fadi hakan a wata zantawa da manema labarai suka yi da shi a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba a Abuja.

A cewar tsohon gwamnan jihar Legas din, ‘yan kasa za su zabi jam’iyyar da ta cika musu alkawuran da ta dauka, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

“Wasu daga cikin gwamnonin jihohin da muke tunanin mutane ba za su zabemu ba sun fara dawowa jam’iyyarmu.

“Don rike kujerunmu a 2023, wajibi ne mu cika alkawuran da muka daukar wa mutane, don su kara zabar mu.

“Hakan shine gaskiya, ba wai siyasa ba. Idan mutum yace zai yi, ko da bai yi dari bisa dari ba, a kalla idan aka ga yana kokari, za a yarda da cewa ka fara ayyuka,.

“Ya kamata a ce jam’iyyar da ke adawa damu, ta fi mu irin wannan tunanin don cin nasara a kanmu.

Yanzu haka ba su yin irin wannan tunanin, kuma ba zan koya musu yadda za su yi ba,” a cewarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here