Yakubu Gowan: Abinda Tsohon Shugaban Kasan Najeriya ya yi

Wani ‘Dan Majalisar Birtaniya ya zargi Janar Yakubu Gowon da laifin sata.

‘Dan Majalisar ya ce tsohon Shugaban kasar ya saci kudi daga asusun CBN.

Babu abin da zai iya tabbatar da wannan magana da ‘Dan siyasar Turan ya yi.

Wani ‘dan majalisar kasar Birtaniya, ya fito ya na ikirarin cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Yakubu Gowon, ya saci kudin al’ummarsa.

‘Dan majalisar ya bayyana wannan ne gaban wani zaure, inda ya jefi Janar Yakubu Gowon mai ritaya da laifin awon gaba da rabin kudin CBN.

Ya ke cewa “Mun san yadda Janar Yakubu Gowon ya yi awon-gaba da rabin dukiyar da ke cikin babban bankin Najeriya (CBN), ya tsere Landan.”

Wannan ‘dan majalisa bai kawo wasu hujjoji da za su gamsar da abin da ya yi da’awa ba, ya nuna rade-radi ya samu, ya ce: “Kamar yadda ake fada.”

Sannan ya cigaba da cewa: “Mun san cewa a cikin birnin nan namu, abin ban haushi, akwai wasu dasu ka lamushe kudin mutanen Najeriya da aka sace.”

“Mun san ana amfani da bankunanmu wajen wannan aiki (wawuran dukiyar sata), don haka Ingila na da damar huro wuta a kan masu sace kudin Najeriya.”

A nan ma wannan mutumi da Legit.ng ba za ta iya tantancensa ba, bai ambaci sunayen mutanen da su ke zaune a kan kudin talakawar Najeriyar ba.

Ko da cewa Najeriya ta samu makudan kudi a lokacin da Janar Yakubu Gowon ya yi mulki tsakanin 1966 – 1975, babu hujjar ya yi sata daga CBN.

A lokacin da aka kifar da Gowon daga mulki ya na Uganda, kuma daga nan ya zarce zuwa Ingila, amma ba a zarge shi da satar kudin bankin CBN ba.

A ranar 19 ga watan Oktoba, 2020, Janar Yakubu Gowon ya cika shekara 86 da haihuwa. A dalilin haka ne mu ka kawo gajeren tarihin tsohon shugaban.

Gowon ya yi karatu a makarantar sojoji ta Royal Military Academy Sandhurst, Ingila, Staff College, Camberley, da kuma Joint Staff College a garin Latime.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here