Dole ne a Matsayina na Jagora na Nemo Hanyoyin Magance Tsaro a Yankin Geidam – Gwamna Buni
Gwamna Buni ya gana masu ruwa da tsaki don tabbatar da zaman lafiya a yankin Geidam.
Gwamnan ya tattauna da shugaban hafsoshin tsaro kan mafita mai dorewa ga lamarin tsaro.
Gwamnan ya bayyana cewa, dole ne a matsayinsa na jagora ya nemo hanyoyin magance tsaro
Gwamnan jahar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, a ranar Lahadi ya gana da shugaban hafsoshin tsaro Janar Leo Irabo don tattauna batun harin Boko Haram a Geidam.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na harkokin yada labarai ga Gwamnan, Mamman Mohammed ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, Vanguard News ta ruwaito.
Read Also:
Mohammed ya ce, tun daga ranar Juma’a ne Buni ya kasance yana tattaunawa da jami’an tsaro don samar da mafita mai dorewa game da kai hare-hare a kan Geidam da al’ummomin kan iyaka.
Gwamna Buni ya ce akwai bukatar gaggauta samar da mafita ta din-din-din game da kutsen da masu tayar da kayar baya ke yi a cikin jahar.
“Matsalar da muke da ita ita ce motsawar masu tayar da kayar baya daga gabar Tafkin Chadi zuwa cikin jahar.
“Muna bukatar duba wannan lamarin gaba daya don magance matsalar din-din-din,” in ji shi.
Ya koka da cewa mutanen Geidam sun sha fuskantar hare-hare da dama da kuma wahalhalun da ba za a iya fada ba wanda ya zama dole a dubesu da idon tausayawa.
Gwamna Buni ya ce “A matsayina na jagora, dole ne in binciko duk hanyoyin da suka hada da ganawa da Shugaban Hafsoshin Tsaro da shugabannin rundunonin tsaro domin tabbatar da tsaro da lafiyar mutanen Geidam da jahar baki daya.”