Kada ‘Yan Najeriya su ɗora wa Gwamnatin Buhari Laifin Rashin Kubutar da Sauran ‘Yan Matan Chibok – Fadar Shugaban ƙasa
Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce kada ƴan Najeriya su ɗora wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari laifin rashin kubutar da dukkan ƴan matan Chibok da aka yi garkuwa da su.
Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkar yaɗa labarai, Femi Adesina, shi ya bayyana haka yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a cikin shirin Sunrise Daily yau Alhamis.
“A 2015, mun san yadda Najeriya take, a yau kuma mun san inda muke. An yi garkuwa da ƴan mata 267, kusan 57 sun tsere nan take sannan gwamnati ta dawo da sama da 100,” in ji Adesina.
Read Also:
Ya ce waɗanda suka rage ba su fi 90 ba, kuma suma suna da hakki na kuɓutar da su domin dawowa gida.
“Sai dai, idan gwamnati ta zo kan mulki lokacin da aka sace ƴan matan kuma gwamnati mai ci ba ta iya bin diddigin ina aka kai su ba, to ba za ka ɗora wa sabuwar gwamnati laifin rashin dawo da su ba, hakan bai kamata ba. An sace ɗaliban Sakandiren Dapchi a lokacin gwamnatinmu, an dawo da su a cikin mako ɗaya in ban da guda biyar ba ciki har da Leah Sharibu,” in ji Adesina.
Mai baiwa shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai ya ce gwamnati na ɗaukar tsauraran matakai wajen dakile ayyukan masu garkuwa a duk lokacin da aka samu afkuwar hakan, inda ya ce gwamnati mai zuwa ma ta ɗauki nauyi wajen ganin an ƙara kuɓuto da sauran ƴan matan.
Ya ce ya kamata a gode wa gwamnati mai barin gado kan irin ci gaban da ta kawowa ƙasar.