Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo ya Samu Karin Matsayi Zuwa Mataimakin Farfesa

 

Yan kwanaki bayan samun sabon matsayi, Dr Sani Umar Rijiyar Lemo ya zama Farfesa.

Dakta Sani na cikin jerin manyan Malaman da jami’ar ta yiwa karin girma.

Mutane da dama sun taya Malamin murna da san barka.

Kano – Jami’ar Bayero dake jahar Kano ta karawa shahrarren Malaman addinin Musulunci, Dakta Sani Umar Rijiyar Lemo matsayi zuwa na mataimakin Farfesa, rahoton Aminiya.

A cewar rahoton, Dr Sani wani Malami ne a tsangayar Adabi da Ilimin Addinin Musulunci a jami’ar ya samu karin matsayi ne bisa gudunmawarsa a bangaren ilimi da bincike.

Wannan na zuwa ne yan kwanaki bayan nada shi shugaban cibiyar nazarin addinin Musulunci da muhawarar addinai a jami’ar BUK.

Bayan Dr Umar Sani, akwai wasu Malamai da jami’ar ta karawa matsayi daga manyan Lakcarori zuwa mataimakan Farfesoshi.

Hakazalika wadanda aka karawa matsayi zuwa cikakkun Farfesoshi.

Daga cikin sauran Malaman da aka karawa matsayi zuwa mataimakin Farfesoshi sun hada da:

1. Umar Sani Fagge – Sashen Larabci

2. Aliyu Harun – Sashem Ilimin Addinin Musulunci

3. Nura Sani – Ilimin Addinin Musulunci

4. Ahmad Salisu – Larabci

5. Matabuli Shehu Kabara – Larabci

Daga cikin wadanda aka yi wa karin girma zuwa farfesa su ne:

1. Shehu Ahmad – Harshen Larabci

2. Usman Sani Abbas – Ilimin Addinin Musulunci

3. Sani Ayagi – Ilimin Addinin Musulunci

4. Umar Abdulkadir – Ilimin Addinin Musulunci.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here