Lagos: Jami’an Hukumar DSS Sun yi wa Ofishin EFCC Dirar-Mikiya
Jami’an hukumar ƴan sandan ciki ta Najeriya DSS sun yi wa ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa a Lagos dirar-mikiya inda suka hana jami’an na EFCC shiga ofishin a Ikoyi.
Kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito cewa daman akwai sabani a tsakanin hukumomin biyu a kan wadda a tsakaninsu ta mallaki ginin.
Read Also:
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wani jami’in DSS ya fada mata bisa sharadin boye sunansa cewa daman sun dade suna takaddama da EFCC a kan wadda ta mallaki ginin, wanda su DSS ne suke amfani da shi tun ma kafin a kirkiri EFCC kuma ya ce an mallaka wa DSS din.
Jami’in ya kara da cewa batu ne da yake a tsakanin hukumomin biyu, kuma bai je gaban shari’a ba sannan ba su taba rikici a kai ba kafin yanzu.
”To amma yanzu ba mu san dalilin da suka zo suka hana jami’anmu shiga ofishin ba, duk da cewa ga sabuwar gwamnati ta zo,” in ji shi.
Jaridar ta ce duk kokarin ji daga bakin masu magana da yawun hukumomin biyu Wilson Uwujaren na EFCC, da kuma Dr Peter Afunaya na DSS a kan batun bai yi nasara ba.