DSS ta yi ƙarin Haske Kan Mamaye Ofishin SERAP

 

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi ƙarin haske kan dalilan da suka sa jami’anta suka mamaye ofishin ƙungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin ƙasa (SERAP) a Abuja ranar Litinin.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Talata a shafinta na intanet, ta yi watsi da rahotannin da ke cewa jami’anta sun kai farmaki ofishin SERAP, inda ta ce ziyarar wani ɓangare ne na bincike da ta saba yi.

DSS ɗin ta jaddada cewa ba daidai ba ne misalta abin da jami’an suka yi a matsayin cin zarafi da kuma tsoratarwa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta cika da tambayoyi da dama dangane da mamaye ofisoshin SERAP da ke Abuja da Legas ba bisa ka’ida ba.”

“Waɗannan bayanan duk ba haka bane ne, kuma idan dai za a iya tunawa, an aike da wata tawaga ta ma’aikatanmu guda biyu bisa doka domin gudanar da bincike na yau da kullum a ofishin SERAP da ke Abuja.”

“Abin takaicin shi ne yadda aka yi kuskuren fassara wannan a matsayin hari da cin zarafi, da kuma tursasa wa jami’an SERAP ba bisa ƙa’ida ba.” in ji sanarwar.

Hukumar ta DSS dai ta buƙaci jama’a da su yi watsi da waɗannan rahotannin da ba su tushe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here