Gwamnatin Najeriya za ta Duba Buƙatun ƙungiyar ƙwadago – Dele Alake

 

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi nazari kan bukatun kungiyar kwadago ta TUC a kokarin dakile yajin aikin da kungiyoyin kwadago ke barazanar shiga a fadin kasar a ranar Laraba, sakamakon cire tallafin man fetur.

Daya daga cikin mahimman bukatun shi ne karin mafi karancin albashi.

Da yake zantawa da manema labarai bayan wani taro da wakilan kungiyar, mai magana da yawun gwamnatin Dele Alake, ya ce tattaunawar ta yi tasiri kuma suna samun ci gaba. Amma kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ba ta cikin tattaunawar.

Mista Alake ya ce “da yawa daga cikin bukatun ba wasu abubuwan da za a iya yi ba ne” amma dole ne a yi nazari a kansu tukuna.

Mataki na gaba shi ne tawagarsa ta gabatar da bukatun kungiyar ta TUC ga Shugaba Bola Tinubu kuma daya daga cikin bukatun shi ne daga wa ma’aikata kafa kan haraji.

A ranar Larabar da ta gabata, masu sayar da man fetur sun kara farashin man fetur zuwa akalla dala 1 ga kowace lita a fadin kasar – karin da ya kai kusan kashi 200%. Hakan ya shafi farashin sufuri da kayan abinci da sauran kayayyaki, yayin da mafi karancin albashi yake kan kimanin dalar Amurka 65.

Dele Alake ya ce gwamnati ta dauki bukatar kara mafi karancin albashi da muhimmanci. Ya ce babu mamaki shugaban kasa zai kaddamar da wani kwamiti da za ta yi nazarin yiwuwar yin karin albashi.

Za a ci gaba da taron a ranar Talata domin bangarorin biyu su duba “alfanu da kuma yiwuwar abubuwan da aka gabatar wa gwamnati.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com