Fassarar Rubutun Ilyasu Ibrahim

January 22, 2019

Ba sai an nanata ba, sanin duk wani xan Nijeriya ne
cewa tun bayan zaven 2015, kuma bayan xarewar Shugaban qasa Muhammadu Buhari
bisa karagar mulki abubuwa da dama, musamman waxanda suka shafi tattalin arziki
sun sukurkuce, talakawa suka rasa tudun dafawa. Haka kuma idan aka koma kan
batun tsaro, wanda yana xaya daga cikin maqusadan kowace irin gwamnati da ke
mulki wato ta kare dukiyoyi da rayukan al’umma daga faxawa cikin tsaka mai wuya
nan ma ba ta canza zane ba, domin kuwa gwamnati mai ci yanzu ta faxi qasa
warwas, kuma har yanzu batun da ake, ta gaza tashi ballantana ma ta kakkave
qasar da  ke gwuyawunta.

To amma ko dama Hausawa sun ce duk wanda ya sayi
rariya ya san tilas za ta zubar da ruwa. Kowa ya san dagar da aka sha da Buhari
da gwamnatinsa a can baya, wato zamanin mulkin sojoji, sai ga shi duk da cewa
yanzu gwamnatin ta dimokuraxiyya ce, amma kamar jiya, i yau, tamkar ungulu ta
koma gidanta na tsamiya ne. Za a iya gane haka daga ire-iren qorafe-qorafen da
al’umma ke yi a kan gazawar gwamnatin Buhari, musamman ma na kusa da shi da
suka haxa har da matarsa, za a iya bada tabbacin cewa gwamnatin ta bai wa
maraxa kunya kuma ba ta da wata alqibla da za ta iya fuskanta ko da kuwa
Shugaban qasa Buhari zai yi mulki shekara dubu, annabi dada.

Ba zai yiwu a iya kattaba ire-iren gazawar shugaban
qasa Buhari da gwamnatinsa ba, amma babba da kowa na ji a jikinsa ita ce ta
fannin tattalin arziki. Ba sai an nanata ba, gwamnati kowace iri ce ita ke da
alhakin tsara manufofinta na tattalin arzikin qasa, waxannan manufofi kuma su
ke jan ragamar al’amurran ci gaban qasa, amma ita gwamnatin Buhari saboda
gwanancewarta, ita ce aka tava yi da ba ta da gwanin ko masanin tattalin
arzikin a cikin masu gudanar da mulkin qasa. Wannan ba komi ya nuna ba sai
gwamnati ce da ba kai, ba gindi, kuma shi ne ya kai qasar nan da talakawa cikin
halin qunci da talauci da ke damuwarta.

Ai tamkar xa ne da iyayensa suka nuna wa so suka
shagwava shi, don haka tilas ya yi abin da ya ga dama, ba tare da shakku ba ko
damuwa da halin qunci da wasu ke ciki.

Saboda haka muddin al’amurran tattalin arziki suka
tavarvare a qasa tilas a samu matsaloli na tashin-tashina ko rikice-rikice ko
da kuwa al’ummar ta cika ta tumbatsa da masana da ‘yan boko, ba za su tava
samun damar kai wa ga gaci a matsayinsu na masu tunani da hangen nesa ba, ko da
kuwa suna da wadatattun kayan aiki, muddin babu tsayayyen tsari na tattalin
arziki da zai yi masu jagora, shirim ba ci ba ne ai!

Wani abin takaicin ban tausayi kuwa (wai matar maye ta
mutu bai ci ba) shi ne, gwamnatin shugaba Buhari ta kasa hango mafita duk da
kasancewar madubin dubarudu a tafin hannunta yake, sai ma dai qara tavarvarcewa
da ta yi a harkokin tattalin arziki wanda a kullum ya ke kwan-gaba-kwan-baya.
Babban qalubalen da irin rashin sanin makama kan jawo shi ne, yakan kawo
lalacewar tattalin arziki, kuma abu ne mai matuqar wuya kafin a gano bakin
zaren nan take. Haka zalika hakan ya yi tasiri ga miliyoyin ‘yan Najeriya duk
da kuwa irin halin juriya da qulafucin da suke nuna wa shugaba Buhari.

Alal misali, idan muka dubi batun hanyoyin sadarwa na
zamani. Gwamnatin shugaba Buhari ce ta umurci kamfanoni sadarwa da su qara
farashin kuxaxin sayen tsarin data. Har wa yau gwamnan babban bankin Najeriya,
Godwin Emelife, ya qara jaddada cewa duk wani kiran waya ko sadarwa da ta wuce
minti uku to tilas a xaga farashin kiran. Ba hauhawar farsashin tsarin sadarwa
na kafafen sadarwa ne kaxai ya zamo wa ‘ya Najeriya qadangaren baki tulu ba,
uwa uba har da hauhawar da kayan albarkatun mai suka yi, wanda  hakan shi ya haddasa tashin gwauron zabin da
kayan masarufi suka yi a  kasuwanninmu,
da suka haxa da kayan albarkatun noma, kamar shinkafa da takin zamani da dai
sauran su. Babu ko tantama gwamnatin ta yi haka ne ba don ciyar da qasa gaba ba
sai don buxe wata kafa ta satar kuxaxe wajen gudanar da harkokin tafiyar da
jam’iyar da ke mulki.

Da wannan sabon tsari musamman na tsadar data da
tsarin kafafen sadarwa, talakan Nijeriya tilas ya gwammace yin awon hatsi a
maimakon sayen katin waya ko tsarin data, don haka ba zai samu damar amayar da
ra’ayinsa ba ko nuna damuwa ko qorafinsa ta waxannan kafafen sadarwar. Wannan
ma wani sabon tsari ne na mulkin kama karya da gwamnatin shugaba Buhari ta
shimfixa cikin ruwan sanyi, ba tare da talakan Najeriya ya ankara ba. Wata
tambayar da ya kamata mu yi kawunanmu kuwa ita ce, shin bayan waxannan hanyoyin
karvar haraji da gwamnati mai ci yanzu ta bijiro da su, nan gaba kuma waxanne
hanyoyin za ta sake zaqulowa, wata qila ma titunan da muke bi za mu fara biya
wa haraji ko ma iskar da muke shaqa, kai hatta gonakinmu da muka gada
kaka-da-kakkani ma sai mun biya masu haraji?

Wata qila ma shi ya sa wani shehun malami mazaunin
qasar Amurka yake da ra’ayin cewa gwamnatin shugaba Buhari gwamnati ce ta jari
hujja, haka zalika duk ginin da aka aza da jari hujja to tamkar an yi gini ne
da toka. Wannan shi ke ba wasu miyagun shugabanni ko ‘yan siyasa kafa don su
lalata tattalin arzikin tare da yin babakere kan wasu muhimman muqamai suna ci
da gumin talakawa. Hasali ma, wannan ne ya sa Hausawa kan ce sai bango ya tsage
qadangare kan samu wurin shiga.

Ga gwamnatin Buhari, jefa tattalin cikin halin ni ‘ya
su bai isa ba, su a gurin su husufin da tattalin arzikin qasa ya shiga hanya ce
ta jefa ‘ya Nijeriya a cikin sabon tasku, shi ya qara bai wa gwamnatin damar
sauya akalar tunani ‘yan qasa, a kullum qaryarsa ita ce an sha wahala kafin a
sami biyan buqata, tir da irin wannan batu nasu. A maimakon gwamnati ta ji qan
talakawa da saka masu shauqi a cikin zukatansu a lokacin da tattalin arziki ke
cikin tsaka mai wuya, sai ya buxe kafa ga wasu miyagun shugabanni a cikin
gwamnati mai ci yanzu, suna qara jefa talakawa cikin qunci da damuwa.

Da a ce gwamnatin shugaba Buhari mai hangen nesa ce,
da ta  hango waxannan matsaloli a
matsayin damarmakin da za ta nuna tausayawarta ga ‘yan Nijeriya; amma sai ga
shi kuma aka sami akasin haka. Haka zalika wani sakarcin da gwamnatin ta nuna
shi ne na rashin tausaya wa ga talakan Nijeriya, ta yadda suka yi qoqarin xaga
darajar naira, amma kuma haqarsu ba ta cimma ruwa ba. Gwamnatin shugaba Buhari
ta shafe tsawon shekara xaya cikin halin husufin tattalin arzikin qasar kafin
ta farga da cewa qudirin nata ba zai yiwu ba a cikin wannan qarnin da muke ciki
na 21. Sun bar naira na ta tamvele ba tare da sun samar mata mazauni ba, saboda
yadda suka kasa suka tsare game da yadda suke so darajar naira ta kasance a
kasuwannin duniya. Wannan sakaci nasu shi ya ba da dama ga cin hanci da rashawa
da almundahana suka yi ta cin karensu ba babbaka tsakanin kasuwannin canjin
kuxaxe.

Daga baya ne suka shafa wa ‘yan canji kashi kaji, suka
kai wa kasuwannin canji farmaki. Daga wannan lokaci ne darajar naira ta faxi
warwas, ‘yan canji suka shiga cin kasuwannin bayan fage. Wannan ya  qara haifar da tumbatsar faxuwar darajar
naira. Bugu da qari, sanin kowa ne cewa matsi da takura ba shi zai sa a samu
sauqin xaga darajar naira ba, hasali ma shi ke qara haifar da kangara da
turjiya daga ma su hada-hadar cinikayyar, musamman ta bayan fage.

Wani batun kuma shi ne ta vangaren albarkatun noma.
Gwamnatin shugaba Buhari ta bakin ministan albarkatun noma Audu  Ogbeh, ya bayyana cewa suna niyyar su sake
dawo da tsohon tsarin nan na hukumomin qayyade farashin albarkatun noma. An
koma gidan jiya ke nan, wai dabara ta qare wa makaxi.

Ba sai an nanata ba gwamnatin shugaba Buhari, gwamnati
ce da ke qudurin mai da wa ‘yan Nijeriya hannun agogo baya, maimakon ta
fuskanci matsalolin rashin guraben ayyukan yi ga matasa, wanda a kullum ake ta
faman rasa aikin yi ga matasa. Wani abin mamaki ma shi ne yadda gwamnatin ta
umurci hukumar qididdiga da ta qididdige yawan marasa aikin yi, wanda hakan ma
shigar burtu ne da gwamnatin ke yi wa ‘ya qasa don ta voye gazawarta.

Babu ko tantama muddin aka sake bai wa gwamnatin
shugaba Buhari damar sake zarcewa a zaven 2019, shakka babu ‘yan Nijeriya za su
qara shiga cikin halin qunci da ba tava ji ko gani ba

Saboda haka muke ganin lokaci ya yi da za a sake lale,
a nemi irin su Alhaji Atiku Abubakar wanda ya taka muhimmiyar rawa, mussaman ta
vangaren hulxar kasuwanci, don haka shi ne mafi cancanta ga zaven 2019, idan
aka yi la’akari da nasarorin da ya samu, wanda hakan ke nuni da cewa yana da
kyakyawan qudiri da hangen nesa wajen farfaxo da tattalin arzikin qasa. Alhaji
Atiku mutum ne da ke da yaqinin cewa al’umma a kowane mataki kan iya ceto kanta
daga tavarvarewar arziki, don haka ya dage tuquru wajen taimakon matasa don su
tsaya da duga-dugansu, haka zalika ya yi imanin cewa gwamnati tana da irin tata
rawar da za ta taka wajen warware matsalolin tattalin arziki musamman ganin
cewa ‘yan Nijeriya mutane ne da ke da saurin karvar canje-canjen da za su iya
kawo sauyi da zai yi tasiri a rayukansu 
cikin walwala, don haka a shirye yake don ya bada irin tasa gudunmuwar
wajen havvaka tattalin arzikin qasar Nijeriya. 

Ilyasu Ibrahim ya rubuta
daga Abuja

The post Dubarudun tattalin arziki Buhari da cancantar zaben Atiku appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here