Cutar Annobar Ebola ta Sake Barkewa a Uganda
Wani matashi da ya kamu da cutar ebola a kasar Uganda ya rasu, yayin da jami’an lafiya suka tabbatar da sake barkewar wannan annoba.
Ministan lafiyan Uganda ya fada wa manema labarai cewa matashin dan shekara 24 ya nuna alamomin cutar ebola kafin ya ce ga garinku nan.
Ba a dai bayyana sunan matashin ba, mazaunin kauyen Ngabano a lardin Mubende mai nisan kilomita 147 daga babban birnin Kampala.
Read Also:
Wata sanarwa ta ambato Cibiyar Binciken Kwayoyin Cutar Bairos ta Uganda da Hukumar Lafiya ta Duniya na cewa cutar wadda nau’in da ake gani nan da can ne a Sudan ta kuma bulla a Uganda.
Mutum takwas ne aka gano da wasu alamomin da ake zargi na kwayar cutar ebola ce in ji sanarwar, kuma yanzu haka suna ci gaba da samun kulawar jami’an lafiya, a daidai lokacin da take shirin aika jami’ai zuwa yankin da lamarin ya shafa.
A 2012 ne kasar wadda ke Gabashin Afirka ta ba da rahoton karshe na samun cutar ebola, kafin dawowar ta a yanzu.